A ranar 3 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da sanya karin haraji na kaso 10% a kan kayayyakin da take shigowa daga kasar Sin, biyowa bayan haraji na kaso 10% da ta kakaba wa kasar a watan da ya gabata. A wannan ranar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kuma tabbatar da fara aiki da matakan da a baya ya sanar na sanya karin haraji na kaso 25% a kan kayayyakin da take shigowa daga kasashen Mexico da Canada a ranar 4 ga wata. Sai dai sakamakon haka, babban mizanin wasu muhimman hannayen jari ya sauka matuka a kasuwar hannayen jari na Amurka, ciki har da DJIA da SPX da kuma IXIC, a yayin da mizanin VIX da ke auna yanayin damuwa da tashin hankali a Wallstreet ya yi tashin kwauron zabi.
Shugaba Donald Trump kullum yana kallon haraji a matsayin matakin da zai iya tilasta wa kamfanoni maido da masana’antunsu cikin Amurka, don farfado da masana’antu da ma samar da guraben ayyuka a cikin gida. Sai dai in mun yi la’akari da abubuwan da suka faru a wa’adin shugabancinsa na farko, za mu gano cewa, bai ci burinsa ba. Dalilin hakan kuma shi ne Trump ya wuce gona da iri kan kintacen tasirin da karin haraji zai yi. Dunkulewar tattalin arzikin duniya bayan yakin duniya na biyu, ta sa akasarin masana’antu sun barbazu a sassan duniya daban daban, ga shi kuma fasahohi da ilmi da ma ababen sufuri da sauransu sun kasance tushen masana’antu na zamani, wadanda ke bukatar a shafe shekaru gommai wajen raya su. Don haka, matakan haraji ba za su iya kawar da matsalolin tushe na dakushewar masana’antu a kasar Amurka, a maimakon haka kuma, za su kara kudin da kamfanonin kasar suke kashewa da ma kudin da al’ummar kasar ke biya, wanda hakan zai kara tsananta matsalar hauhawar farashin a cikin gidan kasar.
- Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su
- Ƴar Majalisar Dattawa Natasha Akpoti Na Fuskantar Dakatarwar Wata Shida
Kafofin yada labarai da dama na cikin gidan Amurka ma sun bayyana damuwarsu game da illolin da matakan haraji ka iya haifarwa. Kafar CNN ta ce, matakan haraji na cusa karin matsaloli ga tattalin arzikin kasar. Ta ce, matakan haraji za su kara kudin da al’ummar kasar ke biya, tare da kara matsawa kamfanonin kasar, wadanda ke fuskantar karin kudin da za su kashe da ma daina odar kayayyakinsu daga ketare.
Bayan da Amurka ta sanar da sanya karin haraji, kasashen Canada da Mexico da ma Sin dukkan sun dauki matakan ramuwar gayya. A ranar 4 ga wata, bi da bi ne ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ma kwamitin kula da dokokin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar sun sanar da jerin matakai na tinkarar matakan haraji na Amurka. Kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin ya kuma jaddada cewa, nuna fin karfi ba shi da amfani da kasar Sin, kuma matsawa da barazana ba hanya ce ta cudanya da kasar. Hakikanin abubuwan da suka faru a shekarun baya ma sun shaida yadda kasar Sin ke mai da matsawa da aka yi mata a matsayin karfin da ke sa ci gabanta, bisa ga juriyar masana’antunta da kirkire-kirkiren fasahohi da ma hadin gwiwarta da sassa daban daban, har ma ta yi ta murkushe makircin Amurka.
A hakika, al’ummar kasar Amurka suna sane da me matakan haraji da Trump ya dauka za su haifar musu. Kamar yadda wani dan kasar ya ce, “idan an samu hauhawar farashi na kaso 25%, mu kanmu ne za mu biya kudin, a maimakon gwamnati ko mutanen kasar Mexico.” Abin hakan yake, duk da cewa matakin haraji ya lalata dokokin cinikin kasa da kasa tare da haifar da rashin tabbas ga farfadowar tattalin arzikin duniya, amma daga karshe, kamfanonin kasar Amurka da ma al’ummar kasar ne za su dandana kudarsa. Daidai kamar yadda Ben Ayers, masanin ilmin tattalin arziki na kasar Amurka ya ce, “Karin iyalai a Amurka za su kara kimtsa wa shiga yanayin tattalin arziki mara tabbas da za su fuskanta a shekarar 2025.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp