‘Yan Nijeriya daga sassa daban-daban a ranar Asabar sun wa wasu hanyoyin birnin New York fenti mai launin tutar Nijeriya sannan suka gabatar da faretin murnar cikar Nijeriya Shekaru 62 da Samun ‘yancin kai.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugabannin al’ummar Nijeriya mazauna Amurka da wakilai sun bi sahun wasu ‘yan Nijeriya domin rufe wasu sassan titin Second Avenue na Midtown na wani dan lokaci.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci faretin akwai jakadan Nijeriya a Amurka, Dr Uzoma Emenike da wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande.
Magajin garin New York, Eric Adams, da karamin jakadan Nijeriya a birnin New York, Amb. Lot Egopija da dan majalisar dokokin Amurka na farko dan Nijeriya, Adeoye Omolewa, suma sun bi sahun masu taya murna a faretin.
Har ila yau, wani matashi mai hazaka mai shekaru 12 mai suna Saxophonist Temilayo Abodunrin, yana cikin ’yan wasan da suka jagoranci faretin.