Wata gobara da ta tashi a unguwar Madina da ke birnin Bauchi, ta yi sanadin mutuwar wasu yara mata biyu, Zainab Bashir Mohammed mai shekaru takwas da Ummu Salma Bashir Mohammed mai shekaru biyar.
Sai dai rundunar ‘yansandan jihar, ta ce gangancin iyaye na barin yara su kadai a gida tare da yin wasa da kayan wuta ne ya haddasa gobarar.
Rundunar ‘yansandan jihar, cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ta samu kiran gaggawa a ranar 17 ga watan Maris, 2024, inda aka sanar da ita tashin wuta a yankin.
- ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sace Mutane 87 A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Kaduna
- Shugaban Jamhuriyar Congo: Ra’ayin Sabon Mulkin Mallaka Ba Shi Da Tushe
Rundunar ‘yansandan tare da jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya sun garzaya wajen da gobarar ta tashi domin kai dauki.
Sai dai kafin zuwa jami’an gobarar ta riga ta rutsa da yaran biyu.
Zafin wutar ya kone yaran ta yadda ba a iya gane gawarwakinsu.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya tabbatar gangaci ne ya haddasa tashin gobarar.
Ya gargadi iyaye da su zama masu taka-tsan-tsan wajen amfani da kayan girki da kuma kayan wutar lantarki.