Magidanta da dama a Jihar Legas da sauran wasu jihohin wannan kasa, sun samu sauki; biyo bayan faduwar farashin Tumatar da kashi 90 a cikin 100.
Hakan ya faru ne, sakamakon noma shi da aka yi da matukar dama, musamman a jihohin da aka fi yawan nomansa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
- Ba Mu Amince Da Yi Wa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Shari’a A Sirrance Ba
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, yanzu duk farashin kwando daya mai nauyin kilo 50, ana sayar da shi kasa da Naira 10,000 zuwa Naira 12,000, ya danganta da irin kyawunsa.
Misali, a Jihar Legas, yanzu ana sayar da kwandonsa a kan Naira 14,000, sabanin yadda a 2024 aka sayar da kwandon nasa a kan Naira150,000.
Wannan ya nuna a zahiri yadda farashinsa ya fadi warwas, cikin wata takwas da suka wuce.
Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25 yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500.
Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa.
A cewar tata, tarin yawan nasa ne ya sa aka samu faduwar farashinsa a kasuwanni, wannan dalili ne ma ya sanya, don gudun kada manoman su yi asara; suke sayar da shi kan farashi mai sauki.
“Daga watannin Janairu, Fabrairu zuwa Maris; ana samun kwantan Tumatir, yanzu kuma muna da injinoni masu kyau na sarrafa Tumatirin, wanda hakan zai sa a samu raguwar farashin”, in ji Zuntu.
Har ila yau, Zuntu ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama, domin sayen Tumatirn da yawa, kafin daga nan zuwa watan Afrilu.
“Akasari mukan bai wa masu amfani da kayan amfanin gona shawarar cewa, su sayi Tumatirin da dama a irin wannan lokaci, don adana shi”, a cewar ta Zuntu.