ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

by Sani Anwar
2 months ago
Lamid

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi korafin cewa, an ki sayar masa da fom din neman takarar shugabancin jam’iyyar PDP, yayin da ya je saya a ranar Litinin da ta gabata.

Duk da haka, tsohon gwamnan ya ce; babu gudu babu ja da baya a kan yunkurinsa na tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar ta PDP, duk da rashin samun damar mallakar fom din tsayawa takarar da ya yi.

  • Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa
  • Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnonin jam’iyyar PDP suka ayyana tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dantakarar shugabancin jam’iyyar, ba tare da hamayya ba daga yankin Arewa maso yamma, Duk da cewa dai, manyan jiga-jigan ‘dan jam’iyyar a yankin sun yi watsi da ayyana hakan.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, uwar jam’iyyar ce dai ta amince da mika wa shiyyar mukamin shugabancin jam’iyyar, amma da sharadin sai an tuntubi masu ruwa da tsaki a yankin.

Ko shakka babu, wannan na kara fito da rikicin da ke jam’iyyar ta PDP a fili, musamman gabanin dan makwanni kadan ta shirya babban taronta na kasa a watan Nuwamba mai zuwa, wanda ke cike da takaddama a ciki.

LABARAI MASU NASABA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

A zantawar Sule Lamido da BBC, ya bayyana cewa; an yi masa kora da hali a hedikwatar jam’iyyar ta PDP.

Ya kara da cewa, ya je hedikwatar jam’iyyar PDP ne; domin karbar fom na takarar shugabancin PDP, sai ya samu ofishin da ya kamata ya karba a kulle, da ya tambaya sai aka ce da shi, a hannun gwamnan Adamawa kadai zai samu fom din.

Lamido ya ci gaba da cewa, ba ya fata a kai ga matakin da za a hana shi shiga takarar, “domin ina tunanin rigimar cikin gida ce, sannan kuma za mu iya samun maslaha a cikin gidan. Amma idan hakan bai yiwu ba, daga nan kuma na san me zan yi,” in ji shi.

Haka zalika, Sule Lamido ya ce; a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar a zaben da za a yi lokacin babban taron jam’iyyar a watan Nuwamban wannan shekara a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Bugu da kari, Lamidon ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ki sayar masa da fom din tsayawa takarar.

Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa; tuni tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki ya yanki nasa fom din, a daidai lokacin da aka ki sayar wa da tsohon gwamnan na Jigawa fom din takarar shugabancin jam’iyyar ta hamayya, wato PDP.

Har wa yau, Jam’iyyar PDP ta sanar da dage tantance dan takara daga ranar Talata zuwa wani lokaci nan gaba, duk da cewa; jam’iyyar ba ta fadi dalilin yin hakan ba.

Haka nan, sanar da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dantakarar maslaha daga Arewacin Nijeriya ya bar baya da kura, inda wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yammacin kasar, shiyyar da Turaki ya fito suka yi watsi da matakin da gwamnoni suka dauka.

Kazalika, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato, Muhammad Bello Aliyu na cikin shugabannin da suka yi fatali da matakin da gwamnonin suka dauka, saboda a cewarsa, ba a ba su damar zama su tattauna ba, gabannin tsayar da Turakin. Kana kuma, an sake samun wasu jiga-jigan jam’iyyar daga Jihar Kebbi da suka yi fatali da wannan maslahar.

Dangane da wanan sabuwar rigima ko rikici, malami a kwalejin ilimi ta share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Dakta Kabiru Sa’id Sufi ya ce; ana neman fama karaya ne a yunkurin gyara targade.

“Mun dauka cewa, tunda aka zo batun zaben shugabanci, matsalolin da jam’iyyar ke ciki sun kusa zuwa karse, musammman ganin har an yi kokarin rarraba mukamai zuwa shiyya-shiyya, amma kuma sai hakan ya bar baya da kura.

“Yanzu haka, an fara samun korafi daga bangarori da dama, ciki har da daga wadanda ake ganin ba su da wata matsala.”

Haka nan, ya kara da ce; hana Sule Lamido sayen fom din takarar shugabancin jam’iyyar, wani babban al’amari ne, domin kuwa a cewar tasa; hakan ya kara haifar da rashin gamsuwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya ce, “Akwai da ma wasu da suke ganin an lasa musu zuma a baki a Arewacin kasar na tsayawa takara, sai daga baya suka gane cewa, ba da gaske ake ba. Idan aka duba, za a ga akwai rashin gamsuwa daga bangarori da yawa. Ko bangaren Shekarau ma, sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al’amuran.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.