Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa ya bayyana cewa duk wani yarfen siyasa da zarge-zarge da da cin mutunci da ake yi masa ana yi ne saboda yadda ya tsaya kai da fata wajan ganin ya tsare mutuncin gwamnatin Masari.
- Idan Buhari Bai Taimaki Tinubu Ba, Bai Kamata Ya Yake Shi Ba Don Ya Taimake Shi —Rarara
- Kwamitin tantance ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Yi Watsi Da ‘Yan Takara 10 Cikin 23
Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya furta haka ne a lokacin da yake yi wa dubun-dubatar magoya bayan sa da kungiyoyi da suka taro a ɗakin taro na Katsina motel a karon farko tun bayan faduwar zaɓen fidda gwani da ya yi jawabi.
“Amma shigarmu cikin gwamnati dukkan wata matsala da aka ji ko ta ɓata suna ko ta zarge zarge saboda alaƙarmu da gwamnati ce, ba wai dan mu ba, don haka mun tsare mutuncin gwamnati da shuwagabannin ta.”
Ya ci gaba da cewa mutane kuma suna ganin ana faɗin abubuwa iri-iri, da suke cikin gwamnati sun sani ba haka maganganu suke ba, mu ma mun sani ba haka suke ba, kuma abin bai taba samun mu ba, saboda mun san don Allah muke yi.” Inji shi
Haka kuma ya ƙara da cewa shi yanzu godiya yake yi wa Allah saboda ya bashi damar kuma cikin shekaru bakwai da aka yi aiki a wannan gwamnati “an riƙe amana, mun tsare mutuncin gwamnatin, mun tsare mutuncin shuwagabannin ta.” In ji shi.
Idan za a iya tunawa Mustapha Inuwa ya shafe shekara takwas yana adawa da Shema, a nan jihar Katsina ya jagoranci adawa ta shekara takwas, ya ce “muna da mutunci muna da ƙima shi ya sa lokacin da Zaɓen 2015 ya ƙara to duk wani wanda yake sha’awar cin zabe a jihar Katsina da suka danganta kan su da mu.”
“Kullum ina faɗi kuma ba zan daina faɗa ba, sai ranar da wani ya ƙaryata ni, zan daina faɗi, wanda zai ce ni da shi ko ma’aikacin gwamnati ko ɗan kwangil ko ɗan siyasa wanda muka yi hulɗar kuɗin gwamnati wanda na ce a yi wani abu da zan amfana da ya kai naira ɗaya ta hanyar da bai kamata ba, idan akwai na ce ya fito ya gaya wa duniya. An yi a can baya, lokacin da muke rigima da tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema kuma na sake faɗi” Inji Inuwa
Haka zalika Mustapha Inuwa ya ce “idan mutum ya ce zai ci amana, wallahi tallahi ya baka tausai, saboda haka ba a cin amana a yi nasara, ba a yin sharri a yi nasara, to ni na riƙe amana, da yardar Allah duk damar da muka samu zamu ci gaba da riƙe amana.
“Haka kuma duk wanda yake ganin ɗabi’arsa ce ko al’adarsa ce cin amana to ya kuma da kanshi kuma ya tausaya zuri’arshi, saboda shi cin amana ba wai akanka kaɗai yake tsayawa ba, wallahi yana tafiya ga zuri’a ne.” In ji Mustapha