Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Sokoto (SEMA) ta bayyana alhini kan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ranar Lahadi, 17 ga Agusta, 2025 a unguwar Kojiyo, ƙaramar hukumar Goronyo.
Rahoton jami’in SEMA na Goronyo ya nuna cewa jirgin ruwan ya ɗauki fasinjoji kusan 45 lokacin da ya kife. An tabbatar da mutuwar mutane 10, an ceto 6 da ransu, yayin da mutane 29 har yanzu ba a gansu ba. A halin yanzu, ana ci gaba da aikin ceto da bincike.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Rahoton farko ya nuna cewa cunkoso da lodin wuce ƙima na ɗaukar fasinjoji na iya zama sanadin hatsarin, matsalar da ta saba faruwa a ƙauyukan da ke kewaye da kogin jihar.
Gwamnatin Jihar Sokoto tare da SEMA da sauran hukumomi sun tura ƙungiyoyin agaji domin ƙarfafa aikin ceto, tare da yin ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa. SEMA ta kuma yi kira ga al’umma su kiyaye dokokin tsaron lafiya musamman gujewa cunkoso a jiragen ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp