Hadarin Mota ya ci rayukan Mutane 19 a kan titin Yangoji zuwa Gwagwalada, inda kuma mutum 8 suka samu munanan raunuka.
Mukaddashin hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Mista Dauda Biu ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce, ya afku ne a jiya Lahadi.
Biu, wanda ya shedawa kamfanin dillancin labarai na kasa afkuwar hadarin a lokacin da ya ziyarci inda abin ya afku ya ce, lamarin ya rutsa da motoci uku kirar bas Toyota Hiace mai lamba MUB- 30 LG da mai lamba DWR-985 XJ sai kuma wata mota daya.
Ya ce, mutane 31 ne hatsarin ya rutsa da su, wadanda suka hada da, maza 11 mace daya sai kuma 19 da suka kone kurmus.
Biu ya kara da cewa, bincike ya tabbatar da cewa, mugun gudu ne ya yi sanadin hatsarin da kokarin wuce juna.
Ya ce, bas ta biyu ce ta doki ta farko daga baya, nan take motocin biyu suka kama da Wuta. A cewarsa, motar ta taho ne daga garin Takai da ke jihar Kano ta nufi Jihar Benin.
Ya ce, akwai motar kirar Citroen da ta yo dakon abincin kaji daga Zaria da ke jihar Kaduna, inda ta nufi jihar Akwa Ibom.
Ya ce, ‘yansanda sun fara tuntubar mahukunta kan bizne gawarwakin 18
Ya ce, wadanda suka samu raunuka an kai su Asibitin Kwali don Cigaba da duba lafiyarsu, sai wata Gawa daya da aka iya gane ta, an kaita dakin ajiye gawarwakin da ke babban Asibitin Kwali Abuja.
Biu ya gargadi masu ababen hawa da su guji yin mugun gudu su kuma dinga kiyaye ka’idojin yin tuki.