Gwamnatin Jihar Adamawa a ranar Juma’a ta ce jihar ta samu rahoton bullar cutar kwalara inda mutane 197 suka kamu, tare da mutuwar mutane biyu a kananan hukumomi shida da ke jihar.
Darakta a ma’aikatar lafiya ta Jihar Adamawa Dakta Celine Laori ce ta bayyana hakan a wata hira da aka yi da ita a Yola.
- Daraktocin Da APC Ta Kora Sun Yi Zargin An Handame Biliyoyi A Jam’iyyar
- Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi
A cewarta, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Shelleng, Guyuk, Yola North, Yola South, Numan da Girei, inda ta kara da cewa an samu rahoton mutuwar mutane biyu a Guyuk da Shelleng.
Laori ta ce gwamnati ta shiga tsakani tare da samar da magungunan da suka dace da sauran matakan rigakafi da magance cutar a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Ta ce duk da haka ta ce wadanda abin ya shafa suna karbar maganin kashe kwayoyin cutar da kuma maganin sake dawo da ruwan jikinsu don samun ingantacciyar lafiya.
“Mun tura kwararru a cikin wadannan al’ummomin don karin daukar rahoto,” in ji ta.
Misis Laori ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kiyaye tsafta da tsaftar muhalli, kuma su guji yin bayan gida a fili.