Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da ke bai wa kowa damar aiko da sakonnin gaishe-gaishensa zuwa ga ‘Yan Uwa da Abokan arziki, na kusa dana nesa.
Barkanku da wannan rana ta Juma’a da fatan kowa zai yi juma’a lafiya,ko kuma fatan an sakko lafiya.
- Ba Mu Taba Ganin Ambaliyar Ruwa Mafi Muni A Nijeriya Kamar Ta Bana Ba – Gwamnati
- 2023: Ba Mu Nada Janar Bamaiyi A Matsayin Daraktan Yakin Zaben PDP A Kebbi Ba – Jam’iyyar
Kafin na je ga sakonni masu karatu zan fara mika sakon barka da juma’a ta zuwa ga ‘yan’uwana da abokanaikina, Sakon barka da juma’a zuwa ga Editana Abdulrazak Yahuza Jere tare da sauran ma’aikatan wannan gida na Jaridar Leadership Hausa baki daya.
Sakon Barka da Juma’a ga Fadila Aliyu Musa, da ‘Yan tawagar Shafin Taskira fatan kowa yana cikin koshin lafiya, fatan kuma an yi sallar juma’a lafiya.
Yanzu kuma zan je ga sakonnin da
Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa mai tarin albarka, tare da fatan Allah ya daukaka wannan gidan jarida tamu, nake mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokan arziki kamar su Salis Kalifa Baba Ahmad, sai kuma babban aminina wato Muhammad wanda aka fi sani da Mamman a cikin garin Kaduna, da kuma Barista Muhammadu Tasi’u Sirajo, da Yunus Abubakar da ke Kaduna, sai Malam Uwaisu Buhari Imam a Abuja, da kuma Muhammad Idris a Lake Biew Homes Phase 2 a Kado, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga mai gidana Raji Musa Yakubu. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Falalu Abdullahi, Zariya. 07032933355
Salam, ina farin ciki tare da godiya ga wannan fili na Goron Juma’a, ina so a mika gaisuwar Goron Juma’a ga yarana Zainaf Ahmad, tare da Adam Ahmad, sai kuma Sadik Ahmad, da Halima Ahmad, sai Yusuf Ahmad, da Maimuna Ahmad, tare da Siyama Ahmad, sai Uwar Gida sarautar Mata Madam Suwaiba, da kuma Nasiru wanda ya tafi Saudiyya da iyalansa, tare da Sa’idu Gulu a karamar hukumar Rimin Gado a garin Kano, sai kuma Alhaji Nura a karamar hukumar Kabo, da Isa Reza a garin Masanawa Kabo, da kuma Yakubu Garo, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Majidadin Kofa Bala Ibrahim. Dafatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin.
Daga Shugaba Ahmad Namalan Kazode, karamar hukumar Kabo. 08034041022
Gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokanai na kamar haka Muhammad Idris, sai kuma Kalifa Baba Ahmad, tare da Umar Dogara Inkiya Lauka-lauka, da Adon Wanki watobaban Amir da Muhibbat, Oga Ubale Mai wanki da guga, tare da Zubairu Dogi, daga karshe ina mai mika gaisuwar Goron Juma’a ga Dan Ladi Kalmi. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah yasa haka, amin summa amin.
Daga Salisu Muhammad, Kaduna. 07036824044
Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan fili namu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga masoyana kamar su Alhaji Isa Ibrahim Bida, sai Abba Abdullahi (Baka son tsufa), da Falalu Abdullahi Zaria City, tare da Usman Hamisu Abuja, sai kuma Ibrahim Tukura (Shugaban matasa), da kuma Umar Sani Madaki, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Sulaiman Yusuf mai mata biyu Kadija da Fatima. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Muhammad Idris, Abuja. 07065279510
Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamumai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga makusantana kamar su Alhaji Murnir Wanbai, sai kuma Alhaji Sulaiman Garki, tare da Malam Abdullahi mai sayar da katin waya a Garki, da Alkali Badarawa Kaduna, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Tijjanin Alhaji Nura dake Garki Abuja. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Alkali Nura, Kaduna. 08066844726
Gaisuwa cike da farin ciki nake mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Yusuf Isa, sai kuma Mahmud Bashir, tare da Faisal Sani, da Hauwa Isa, sai Rashida Isa, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Maimuna Isa. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Iliyasu Isa, Abuja. 08169130801
Assalamu alaikun. Fatan alkairi ga LEADERSHIP Hausa, ina mai farin cikin da wannan fali namu da aka bamu dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya daukaki wannan Jarida mai farin jini a Duniya baki daya. Ina so in mika sakon gaisuwar Joron Juma’a ga, manyan abokan karatuna kamar su Tasi’u Sirajo (Barrister), da Yunus Abubakar, tare da Rabi’u Abdullahi (baban Tahir), sai kuma Haruna Ibrahim (Baba), da Zakariyya Umar Wade, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Aliyu Muhammad. Da fatan duk sunanan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Abdulmuminu Sani, Katsina. 08135391867