Mazauna yankin Kubwa da ke babban birnin tarayya, Abuja sun shiga firgici bayan da wani bene mai hawa biyu ya ruguje wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu.
Ginin wanda ake kan gina shi ya ruguje ne a titin Hamza Abdullahi da ke kan titin Gado Nasco.
- Abin Da Ya Sa Ba A Son Yin Wanka In Ana Ruwa Da Walkiya A Birtaniya
- Zulum Ya Ba Da Umarnin Bude Ofishin NNPP Da Aka Rufe A Borno
Jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na ta aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
A cewar NEMA, mutane shida ne lamarin ya rutsa da su.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Manzo Ezekiel, ya fitar, ya ce NEMA ta sanar da faruwar lamarin da misalin karfe 1:00 na rana, inda nan take ta tattara wadanda suka kai daukin gaggawa, wadanda suka hada da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Abuja, hukumar kashe gobara, jami’an tsaron farin kaya da kuma ‘yansanda zuwa wurin.
Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya Abuja (FEMA), Alhaji Abbas Idris, ya sanar a jiya cewa mutane biyu da suka makale a ginin da ya ruguje a Kubwa da ke wajen birnin Abuja, sun mutu.
Alhaji Idriss, ya ce aikin ceto a wurin da ya rufta ya zo karshe tare da ceto mutane biyar da ransu; uku da suka samu raunuka daban-daban yayin da mutane biyu ba su samu raunuka ba.
A halin da ake ciki, karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu, ta jajanta wa iyalan wadanda ginin Kubwa ya shafa.
Hafeez Olayinka, daya daga cikin wadanda aka ceto daga ginin da ya rufta, ya ce ya shafe sa’o’i a cikin tarko.
Olayinka, wanda ya koma inda lamarin ya faru bayan an yi masa jinya a asibiti, ya shaida wa manema labarai cewa ya isa wurin ginin da ya ruguje ne a ranar Litinin.
“Ni da wasu mun makale tun daren Alhamis. Da misalin karfe 11:30 na dare ranar Alhamis.”