Rahotanni sun bayyana cewar wasu mutane biyu sun mutu yayin da da dama suka jikkata a wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Cukuma da ke karamar hukumar Suletankarkar a Jihar Jigawa.
- Sanar Da Taiwan Ganawa Tsakanin Shugabannin Sin Da Amurka Da Amurka Za Ta Yi, Yana Tattare Da Mummunar Manufa
- Dattawan Arewa Sun Yi Tir Da Kalaman Gwamna Ortom Kan Ƙyamar Fulani
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Effiom Emmanuel Ekot, ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ofishinsa.
Ya ce wasu gungun matasa da suka samu raunuka a ranar 08/11/2023 sun kai rahoto ofishin ‘yansanda na Suletankarkar cewa wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai musu hari.
Effiom ya ce an kai wadanda lamarin ya rutsa da su asibiti kuma an yi musu magani daga baya aka sallame su.
Ya bayyana cewa da misalin karfe 4:00 na yamma, hakimin kauyen Ciromawa ya kai rahoto ga ‘yansanda cewa an gano gawarwaki biyu a daji da ke kusa da kauyen.
Ya ce ‘yansanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai gawarwakin biyu zuwa asibiti, kuma likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Effiom ya ce an gano mutum daya kuma an mika gawarsa ga iyalansa wanda tuni suma birne shi.
Ya ce an mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.