Akalla mutane hudu ne aka ruwaito cewar sun rasu a wani hatsarin da ya afku a kauyen Ayere da ke kan hanyar Ilorin zuwa Bode-Saadu a Jihar Kwara.
Rundunar ‘yansandan jihar, ta ruwaito cewar, hatsarin ya afku ne tsakanin wasu motoci kirar DAF guda biyu da misalin karfe 1:02 na rana a kan hanyar Ilorin zuwa Bode Sa’adu.
- Dalilin Da Ya Sa Ban Yi Musabaha Da Gwamna Yusuf Ba – Ahmed Musa
- Goman Ƙarshe Na Watan Ramadan [Darajarsu Da Mutsayinsu] Na 1
A wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na sashen Busari Basambo a Ilorin, ta fitar a ranar Laraba, ta ce: “Da samun rahoton hatsarin da ya faru da misalin karfe 1:09 na rana, nan take jami’an hukumar FRSC suka kai daukin gaggawa wajen, inda suka ceto wasu maza biyar da suka jikkata. Sannan aka kai su asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin.”
Ta bayyana cewa binciken aka gudanar ya nuna cewa daya daga cikin manyan motocin da ke dauke da taki da fasinjoji takwas ta bi hannun da ba nata ba, lamarin da ya kai ta yi karo da wata motar tumatir.
A cewarta: “Mutane 10 ne hatsarin ya rutsa da su. Biyar sun samu raunuka, yayin da wasu hudu suka rasa rayukansu.
“Ya zuwa yanzu an kashe wutar da ta kone motocin, kuma an bude hanyar da hatsarin ya afku domin ci gaba da zirga-zirgar ababen hawa.”