Ana fargabar a ƙalla mutane biyar sun mutu sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya rusa gidaje a ƙauyukan Dalmari da Zindiwa da Kesa na ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.
Wannan na zuwa ne biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama ana yi a ƙauyukan wanda akasarin gidajensu na laka ne, inda ruwan ya lalata gidaje da dama tare da ɓarnata gonaki masu yawa a sassa daban-daban na jihar Bauchi.
- NIS Reshen Bayelsa Ta Raba Ruwan Sha Ga ‘Yan Gudun Hijira A Yenagoa
- PDP Ta Jajantawa Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kebbi
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Gamawa, Adamu Mohammed Udubo, ya tabbatar da cewa wasu gine-gine sun ruguje kan wasu matasa uku a ƙauyen Dalmari wanda hakan ya yi ajalinsu, kana a ƙauyen Zindiwa ma rugujewar ginin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 inda a ƙauyen Kesa wani ɗaki ya rufta kan wata tsohuwa wadda ita ma ta rasu nan take.
Adamu ya ce tun da farko ƙaramar hukumar ta kawo buhunan yashi don shinge wurare masu rauni da ake tunanin ruwa zai iya ambaliya, amma sakamakon yawan ruwan ya yi galaba a kai tare da mamaye garin.