Akalla mutane shida ne, ciki har da wani karamar yarinya, suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Ajue da ke kan hanyar Ondo-Ore a Jihar Ondo.
LEADERSHIP ta samu cewa hatsarin ya afku ne lokacin da direban wata tirela da ta taho daga garin Ondo, motar ta kwace masa daga kan titi inda ya afka kan wata motar kirar Nissan mai dauke da fasinjoji 10.
- Allah Ya Yi Wa Hakimin Rimi A Masarautar Katsina NUHU ABDULKADIR Rasuwa
- An Yi Wa Mawaki Eedris Abdulkareem Dashen Koda
A cewar wata majiya, mutane shidan da ke cikin motar bas din sun mutu nan take.
An kuma bayyana cewa, an yi kokarin ceto wasu fasinjojin da ke cikin motar a lokacin da lamarin ya faru.
Kwamandan sashen Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da ke Ore, Babafemi Alonge, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Alonge, ya ce hatsarin ya rutsa da wata babbar mota mai lamba MUS 321 YF da kuma motar bas kirar Nissan mai lamba RGB 487 XA.
Ya kuma kara da cewa motocin biyu sun yi karo da juna ne sakamakon rashin kula da direbobin ke yi.
A cewarsa, “Hatsarin ya hada da wata babbar mota da wata mota bas kirar Nissan dauke da fasinjoji 10 da suka taho daga Ondo.
“Abin takaici, direban motar da ke kan hanyar zuwa Ore ya rasa yadda zai yi, inda nan take ya shiga layi na biyu ta hanyar kutsawa kan motar bas.
“Mutane shida ne suka mutu a cikin motar bas sakamakon hatsarin, yayin da wasu da suka samu raunuka, jami’anmu sun garzaya da su asibiti.
“Wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun hada da namiji daya, mata hudu babba da yarinya mace yayin da mutane hudu suka samu raunuka.
Sai dai ya kara da cewa an kai gawarwakin mamatan dakin ajiyar gawa.