Hakimin Kauran Katsina kuma Hakimin Rimi (Hakimin Rimi) a jihar Katsina, Alhaji Nuhu Abdulkadir ya rasu.
Basaraken ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina.
- Ruwan-wuta: ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Kubutar Da Dabbobi 110 A Katsina
- Za A Sake Yin Gasar Masu Kirkira Da Fasaha Ta Katsina Karo Na Biyu
Wani cikin Iyalan Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir ya tabbatar da rasuwar basaraken a safiyar ranar Talata.
Talla
Za a yi jana’izarsa da rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kafin rasuwarsa, Hakimin Rimi yana cikin Sarakuna 40 na Masarautar Katsina.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, basaraken ya yi bikin cika shekaru 40 a kan karagar mulkin Rimi kwanan nan.
Talla