• Leadership Hausa
Monday, February 6, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Ondo

by Sadiq
6 months ago
in Labarai
0
Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Ondo

Akalla mutane shida ne, ciki har da wani karamar yarinya, suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Ajue da ke kan hanyar Ondo-Ore a Jihar Ondo.

LEADERSHIP ta samu cewa hatsarin ya afku ne lokacin da direban wata tirela da ta taho daga garin Ondo, motar ta kwace masa daga kan titi inda ya afka kan wata motar kirar Nissan mai dauke da fasinjoji 10.

  • Allah Ya Yi Wa Hakimin Rimi A Masarautar Katsina NUHU ABDULKADIR Rasuwa
  • An Yi Wa Mawaki Eedris Abdulkareem Dashen Koda

A cewar wata majiya, mutane shidan da ke cikin motar bas din sun mutu nan take.

An kuma bayyana cewa, an yi kokarin ceto wasu fasinjojin da ke cikin motar a lokacin da lamarin ya faru.

Kwamandan sashen Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da ke Ore, Babafemi Alonge, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Labarai Masu Nasaba

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

Ko Mafarkin Samun Gwamna Mace Ta Farko A Nijeriya Zai Zama Gaskiya?

Alonge, ya ce hatsarin ya rutsa da wata babbar mota mai lamba MUS 321 YF da kuma motar bas kirar Nissan mai lamba RGB 487 XA.

Ya kuma kara da cewa motocin biyu sun yi karo da juna ne sakamakon rashin kula da direbobin ke yi.

A cewarsa, “Hatsarin ya hada da wata babbar mota da wata mota bas kirar Nissan dauke da fasinjoji 10 da suka taho daga Ondo.

“Abin takaici, direban motar da ke kan hanyar zuwa Ore ya rasa yadda zai yi, inda nan take ya shiga layi na biyu ta hanyar kutsawa kan motar bas.

“Mutane shida ne suka mutu a cikin motar bas sakamakon hatsarin, yayin da wasu da suka samu raunuka, jami’anmu sun garzaya da su asibiti.

“Wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun hada da namiji daya, mata hudu babba da yarinya mace yayin da mutane hudu suka samu raunuka.

Sai dai ya kara da cewa an kai gawarwakin mamatan dakin ajiyar gawa.

Tags: BasFRSCHatsarin MotaKaramar MotaOndoTirela
Previous Post

Girmama Cikakken ’Yanci Da Yankunan Kasa, Wajibi Ne A Kan Kowacce Kasa Babba, Ko Karama

Next Post

Tsarin Tantance Ingancin Rigakafin Sin Ya Kai Sabon Mataki Na Nagarta

Related

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri
Rahotonni

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

4 hours ago
Ko Mafarkin Samun Gwamna Mace Ta Farko A Nijeriya Zai Zama Gaskiya?
Labarai

Ko Mafarkin Samun Gwamna Mace Ta Farko A Nijeriya Zai Zama Gaskiya?

6 hours ago
NAHCON Ta Rarraba Kujerun Aikin Hajjin Bana Ga Jihohi 36 Da Abuja
Labarai

NAHCON Ta Rarraba Kujerun Aikin Hajjin Bana Ga Jihohi 36 Da Abuja

8 hours ago
Matar Sufeto Ta Gurfanar Da Kurtun Dan Sanda A Kotu Kan Kashe Mijinta
Kotu Da Ɗansanda

Ya Kashe Makocinsa Don Ya Haske Idon Mahaifiyarsa Da Cocila

10 hours ago
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kisan Fulani 40 A Jihar Nasarawa
Labarai

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kisan Fulani 40 A Jihar Nasarawa

12 hours ago
Sojoji Sun Kama Mutum 116 Da Ke Yin Laifuka Daban-daban A Legas
Kotu Da Ɗansanda

Sojoji Sun Kama Mutum 116 Da Ke Yin Laifuka Daban-daban A Legas

13 hours ago
Next Post
Tsarin Tantance Ingancin Rigakafin Sin Ya Kai Sabon Mataki Na Nagarta

Tsarin Tantance Ingancin Rigakafin Sin Ya Kai Sabon Mataki Na Nagarta

LABARAI MASU NASABA

Afirka Ba Ta Bukatar Lakca

Afirka Ba Ta Bukatar Lakca

February 5, 2023
Manoman Kwakwa 50 Sun Samu Horo Kan Noman Zamani

Manoman Kwakwa 50 Sun Samu Horo Kan Noman Zamani

February 5, 2023
Sin Na Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Harbo Babban Balan-balan Din Kasar Sin

Sin Na Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Harbo Babban Balan-balan Din Kasar Sin

February 5, 2023
Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

February 5, 2023
Ko Mafarkin Samun Gwamna Mace Ta Farko A Nijeriya Zai Zama Gaskiya?

Ko Mafarkin Samun Gwamna Mace Ta Farko A Nijeriya Zai Zama Gaskiya?

February 5, 2023
Shirin Fim Na Tallata Shagalin Murnar Bikin Kunna Fitilu Da CMG Ya Tsara Ya Jawo Hankulan Al’ummar Afirka

Shirin Fim Na Tallata Shagalin Murnar Bikin Kunna Fitilu Da CMG Ya Tsara Ya Jawo Hankulan Al’ummar Afirka

February 5, 2023
An Gudanar Da Jerin Ayyuka Don Murnar Cika Shekara 1 Da Samun Nasarar Gudanar Da Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi Na Beijing

An Gudanar Da Jerin Ayyuka Don Murnar Cika Shekara 1 Da Samun Nasarar Gudanar Da Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi Na Beijing

February 5, 2023
NAHCON Ta Rarraba Kujerun Aikin Hajjin Bana Ga Jihohi 36 Da Abuja

NAHCON Ta Rarraba Kujerun Aikin Hajjin Bana Ga Jihohi 36 Da Abuja

February 5, 2023
Matar Sufeto Ta Gurfanar Da Kurtun Dan Sanda A Kotu Kan Kashe Mijinta

Ya Kashe Makocinsa Don Ya Haske Idon Mahaifiyarsa Da Cocila

February 5, 2023
Gwamnan Jigawa Ya Nada Hameem Nuhu Sanusi Matsayin Sabon Sarkin Dutse

Gwamnan Jigawa Ya Nada Hameem Nuhu Sanusi Matsayin Sabon Sarkin Dutse

February 5, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.