Rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF) ta kai wani hari kan wata rundunar ‘yan bindiga da ta yi kaurin suna a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, inda mutane 62 da aka yi garkuwa da su suka yi nasarar tserewa.
Sansanin wanda yake a Jigawa Sawai, ya kasance mafakar fitaccen shugaban ‘yan bindigar nan, Muhammadu Fulani, wanda ya addabi al’umomin Matazu, Kankia, Dutsinma a Katsina da sauran sassan jihar Kano.
- Filato Ta Tsakiya Ta Amince Da Tazarcen Mutfwang A 2027
- APC Ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa
Hare-haren da aka kai ranar Asabar da karfe 5:10 na yamma, ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa daga maboyarsu inda dimbin wadanda aka yi garkuwa da su, suka tsere.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Katsina, Dakta Nasir Mu’azu ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa wadanda suka samu kubuta sun kai kimanin mutane 62 bayan da ‘yan bindigar suka tsere saboda harin da jirgin ya kai musu.
Ya yi bayanin cewa, yawancin wadanda suka kubuta, an sace su ne daga kauyen Sayaya yayin wani harin da aka kai da daddare a ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025.
Mu’azu ya kara da cewa, a halin yanzu 12 daga cikin wadanda suka kubuta, ana kula da lafiyarsu a babban asibitin Matazu, yayin da 16 kuma ke cibiyar lafiya fa rundunar sojoji ta ‘Forward Operating Base (FOB)’ da ke Kaiga Malamai domin samun kulawar lafiya ta matakin farko.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya yaba wa kokarin jami’an tsaro tare da jaddada aniyar gwamnati na kawo karshen ‘yan bindiga a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp