Akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar kifewar kwalekwale da kuma nutsewa a ruwa a kananan hukumomin Gwaram da Kaugama da ke Jihar Jigawa.
An ruwaito cewa mutum biyar dai sun rasu ne a kauyen Martaba da ke karamar hukumar Gwaram, inda aka samu nasarar ceto hudu daga cikinsu.
- Magidanci Ya Nemi Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.6 Kafin Ya Sake Ta A Kaduna
- Rashin Kulawa Da Jama’a Ba Dimokuradiyya Ba Ce
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shi’isu Adam, ya cw kwale-kwalen ya kife da mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga masallaci.
“Mutane hudu, da suka hada da wani mai shekara 60 mai suna Barkeji, sun tsira da rayukansu inda aka samu ceto su da ransu,” in ji kakakin.
Ya kuma ce a sanadiyyar gudunmawar da wasu masunta suka kai, an samu gawawwaki biyar da suka hada da wani dattijo mai suna Lukateru mai shekara 60 da Musa mai shekara 50 da Sale mai shekara 50 da Alhaji Shuaibu mai shekara 60 da Dogo mai shekara 50, dukkansu mazauna garin Darazau da ke Jihar Bauchi.
Ya kara da cewa, tuni an mika gawawwakin ga iyalai da ‘yan uwansu domin yi musu jana’iza.
A wani labarin kuma, wasu yara mata uku, sun rasu a sakamakon nutsewa a ruwa a kauyen Faskarau da ke garin Ja’e a karamar hukumar Kaugaman a Jihar Jigawa.
Yaran sun hada da Maryam Salisu mai shekara 10 da Bahayura Lawan, ita mai shekara 10 da kuma Lawisa Sule mai shekara takwas a duniya.
A wata sanarwa da kakakin hukumar tsaro ta NSCDC, CSC Adamu Shehu, ya fitar a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar Litinin, yayin da suka je wanki a rafi.
Ya ce an kai gawarwakinsu babban asibitin Kaugama, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Bincike ya nuna cewar, yaran, bayan sun gama wankin nasu ne suka yanke shawarar yin wanka, lamarin da ya jawo rasa rayukansu.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewar shekaru 20 da suka gabata, an taba samun irin wannan iftila’in inda yara uku mata suka rasu.
Tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan mika gawarwakinsu ga iyalansu.
A nasa bangaren, babban kwamandan rundunar ta NSCDC a jihar, Musa Alhaji Mala, ya jajanta wa iyalan mamatan, gami da jan hankalin iyaye da su kula wajen tura yara rafi, musamman a wannan lokacin da ake fama da ambaliyar ruwa a fadin Jihar.