Aƙalla mutane takwas ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Atura Bus Stop, hanyar Lagos-Badagry, lokacin da wata motar haya ƙirar Mazda mai ɗaukar fasinjoji 16 ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota ƙirar DAF. Hukumar LASTMA ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da rashin iya sarrafa mota daga direban motar hayar.
A cikin wata sanarwa, Daraktan Hulɗa da Jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce hatsarin ya kasance mai muni matuƙa, inda ya kashe direban motar, yaran moto da sauran fasinjoji shida. Ya ce hatsarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da ɗimuwa. Jami’an LASTMA, da FRSC, da rundunar ƴansanda da Sojoji daga Ibereko sun gudanar da aikin ceto cikin gaggawa.
- Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau
- Jami’in LASTMA Na Bogi Da Ya Sato Mota Ya Shiga Hannu
An ceto mutane takwas da suka jikkata, kuma aka garzaya da su Asibitin Gwamnati da ke Badagry don samun kulawar gaggawa. Adebayo ya bayyana cewa hatsarin ya zama darasi, yana mai jaddada cewa gudu, da rashin kiyayewa da sakacin direbobi na ƙara haddasa irin waɗannan hatsarin a tituna.
Babban Manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru, inda ya gargaɗi direbobi su kiyaye gudu da bin dokokin hanya. Ya ce gwamnati ta fara shigar da kayan rage gudu a wuraren da ke da haɗari domin rage yawaitar hatsura. Ya ƙara da cewa dole ne direbobi su nuna kishin ƙasa ta hanyar yin tuƙi cikin hankali da kiyaye lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp