Rundunar ‘yansandan Jihar Filato ta bayyana cewar mutane 96 ne ‘yan bindiga suka hallaka a kauyuka 12 a karamar hukumar Bokkos da wassu 17 a karamar hukumar Barkin Ladi.
A wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ya aike wa manema labarai a ranar Talata, ta nuna cewa ‘yan bindigar da har yanzu ba a san su ba, sun kone gidaje 221, sun kuma kone babura 27 da motoci guda takwas.
- Sin Ta Fitar Da Shirin Kyautata Yanayin Kasuwanci A Yankin Guangdong-HK-Macao Na Kasar
- NNL: An Ci Tarar Kungiyar Mailantarki FC Naira Miliyan Daya Kan Rashin Da’a
Hare-Haren wanda aka fara tun ranar Asabar zuwa Litinin, ya sanya dubban mutane, musamman mata da yara, da suka tsira da ransu, yin gudun hijira.
A jiya Litinin ne, 25 ga watan Disamba, kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa akalla mutane 160 ‘yan bindiga suka kashe a hare-hare daban-daban da suka kai a jihar.
Sai dai wannan hari ya haifar da zazzafar muhawara, inda dubban mutane ke kiran masu ruwa da tsaki kan tsaro da sake kaimi kan yaki da ta’addanci a Nijeriya.