Mutane da dama ne suka kubuta sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyu a Bukuru, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a daren Lahadi.
Wakilinmu ya tattaro cewa ginin da ya rushe, akwai Mutane dake zaune a wani bangare, sannan kuma wani bangare shaguna ne da ake kasuwanci. Ginin yana daura da filin wasa na Bukuru.
A cewar wani mazaunin yankin mai suna Yohana Samson, ya shaida wa LEADERSHIP cewa sun ji kara daga ginin da misalin karfe tara na dare. Mun gode wa Allah da ya kasance ranar Lahadi ce babu kowa a bangaren da ake kasuwanci.
Haka kuma, Nura Musa, wanda shi ne mai kula da ayyukan bincike da ceto na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), shiyyar Arewa ta Tsakiya, ya tabbatar wa LEADERSHIP da afkuwar lamarin.
A cewarsa, ginin mai hawa biyu ya ruguje ne a lokacin da mutanen da ke ciki suka bar ginin saboda sun gano cewa akwai alamun ginin na shirin rushewa a kowane lokaci.
Sai dai ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba a lamarin, inda ya kara da cewa da suka samu labarin faruwar lamarin, NEMA ta yi gaggawar zuwa wurin tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an kashe gobara na jiha da na tarayya da ‘yan sanda da kuma ‘yan kungiyar agaji ta Red Cross don ceto Mutane ko wasu sun makale aciki.