Ma’aikatar harkokin raya al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin, ta fidda bayanin cewa, yayin kwanaki 8 na hutun bikin tsakiyar kaka, da bikin murnar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, mutane kimanin miliyan 826, sun yi tafiye-tafiye domin yawon shakatawa a cikin kasar Sin, adadin da ya karu da kawo 71.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara, kuma adadin ya karu da kaso 4.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2019.
Haka kuma, yawan kudaden shiga da aka samu sakamakon harkokin yawon shakatawar ya kai Yuan biliyan 753 da miliyan 430, adadin da ya karu da kaso 129.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara, kana, adadin ya karu da kaso 1.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019.
A yayin hutun bukukuwan 2, harkokin raya al’adu da yawon shakatawa sun farfado cikin sauri, kuma hada hadar kasuwanni ma ta gudana cikin yanayin karko.
Bugu da kari, hukumar kula da harkokin cin rani ta kasar Sin, ta fidda bayani a yau Asabar, wanda ke cewa, a yayin hutun bukukuwan biyu na bana, adadin mutane da suka yi shige da fice daga kasar Sin, ya kai miliyan 11 da dubu 818, wato a kowace rana, adadin ya kai mutane miliyan 1 da dubu 477, wanda ya karu da kaso 290 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)