Wasu mutane a jihar Bayelsa sun fasa tare da wawushe rumbun tara hatsi da sauran kayan abinci da gwamnatin jihar ta killace a birnin Yenagoa domin raba wa jama’a da zummar rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa tun a 2022.Â
Gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan abincin sun fara lalacewa.
- Yawan Sinawa Masu Amfani Da Intanet Ya Kai Fiye Da Biliyan 1
- Man Girki Mara Asali: Kamfanin Power Oil Ya Kulla Alaka Da Ali Nuhu Kan Wayar Da Kai
An fasa rumbun ne da ke kan babbar hanyar Isaak Boro a Yenagoa saboda irin tashin hankalin da al’ummar ke ciki na hauhawar farashn kayayyakin masarufi wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da ya haddasa tsananin tsadar rayuwa.
Janye tallafin ne ya sa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi daga N190 zuwa 620 kan kowacce lita wanda hakan ya shafi farashin motocin sufuri da kayan abinci da sauransu.
Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa wadannan kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da ingancin da za a iya ci, domin sun lalace don haka duk wanda ya ci zai fuskanci matsala.
Da yake bayani kan mamayar da aka yi wa rumbun ajiyar, babban daraktan hukumar, Hon. Walamam Sam Igrubia, ya ce suna shirin tunkarar ambaliyar ruwa a bana, a lokacin da shugaban hukumar ya ziyarci wuraren, ya kuma tarar da sauran kayayyakin abinci, musamman shinkafa da gari wadanda ba su dace da ci ba.
Wannan shi ne karo na biyu, bayan wawason da jama’a suka yi a jihar Adamawa.