‘Yan sandan birnin tarayya, Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum daya a wani rikici da ya barke a unguwar Gwarimpa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Ade, ta ce rikicin ya barke tsakanin wasu kabilu guda biyu mazauna wani yanki da ake kira ‘Gwarimpa village’.
- Kamar Buhari Da Ganduje: Darius Ishaku Ya Nemi Gafarar ‘Yan Taraba
- Yau Tinubu Zai Dawo Nijeriya Bayan Ya Shafe Kwanaki 34 Baya Kasa
Bayanai sun ce tun ranar Asabar ne tarzomar ta fara bayan kabilar Gbagyi sun yi yunkurin korar wasu da suke zargin suna dillancin kwayoyi a yankin.
‘Yan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi dan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadin raunukan da aka ji masa a ranar Lahadi.
Sun ce rikicin ya sake tashi da safiyar Litinin, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar dan uwan nasu da aka kai asibiti sanadin raunukan da ya ji, ko da yake sun yi kokari, a cewar Josephine sun shawo kan al’amuran.
Ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa Fulani makiyaya ne suka kai hari unguwar Gwarimpa a cikin birnin Abuja.
Wasu kafofin yada labarai sun ba da rahoton cewa fadan kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum uku, zargin da kakakin ‘yan sanda ta ce shi ma babu kanshin gaskiya a ciki.