A cikin awanni 24 kacal, sama da mutane 20,000 sun nemi gurbin aikin mutane 4,000 da gwamnatin Jihar Adamawa ta buɗe.
Hukumar kula da ma’aikatan gwamnati ta jihar ce ta bayyana hakan a ranar Laraba.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Aiki Kan Rigakafin Covid -19
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Cin Zali Ta Hanyar Kakaba Haraji Ya Illata Kimar Amurka
Sakataren hukumar, Abubakar Maiha, ya ce za a yi amfani da cancanta da gaskiya wajen zaɓar waɗanda za a ɗauka aiki, kamar yadda Gwamna Ahmadu Fintiri ya umarta.
“Za mu tabbatar da cewa an gudanar da ɗaukar ma’aikata cikin gaskiya da adalci, kamar yadda gwamna ya umarta,” in ji Maiha a wata hira da ya yi a Yola.
Ya bayyana cewa yawan mutane da suka nemi aikin ya sa dole su inganta tsarin aikin domin a iya ɗaukar waɗanda suka cancanta..
An ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har tsawon makonni biyu.
Bayan haka, za a zaɓi waɗanda suka cancanta domin ganawa da su da kuma tantance su
Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su gaggauta cike fom ɗin domin guje wa cunkoson mutane a ranar ƙarshe.
Gwamna Fintiri ne, ya bayar.da umarnin buɗe shafin domin ɗaukar sabbin ma’aikata 4,000 a aikin gwamnati a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp