Cikin watanni shida a wannan shekarar, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce, akalla mutane 25 masu shekaru 2 zuwa 78 ne suka bace bat a jihar Abia.
Wadanda suka bace din masu shekaru daban-daban sun hada da yara da kuma manya maza da mata.
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Barayin Ragon Layya 2 A Ogun
- Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Tabbatar da Kashe Jami’inta, ACP Aminu Umar
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ne ya shaida hakan a jiya a ofishinsa da ke Umuahia.
Ogbonna, ya ce suna yin iya kokarinsu wajen nemo wadanda suka batan tare da kare sauran jama’a daga shiga hannun bata-garin ‘yan ta’adda a jihar.
Ya shawarci al’umar jihar da su kula da iyalansu domin kare su daga fadawa hannun bata-gari, “kwanan wasu mutane sun ga wata karamar yarinya a makwaftansu inda ta ziyarci saurayinta daga baya iyayenta suka ayyana cewar ta bata, da ta ji hakan nan take ta gaggauta komawa gida.” Cewarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp