A ranar Alhamis wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da mutane 19 a yankin Bwari da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.
Wannan lamarin na zuwa ne kasa da ‘yan kwanaki da mutuwar mutum 30 a sakamakon ruftawar masu hakar ma’adinai ta zama sababi a yankin Kuje da ke cikin birnin tarayya Abuja.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Abuja, Sun Yi Garkuwa Da Mutane 9
- ‘Yan Bindiga Na Shirin Sake Kai Wa Jirgin Abuja Zuwa Kaduna Hari – DSS Ta Yi Gargadi
Ministan babban birnin tarayya l, Nyesom Wike, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da shugabannin yankuna shida na Abuja.
Ministan wanda ya nuna mamakinsa da matakin, ya ce, zai gayyaci daraktan hukumar tsaron farin kaya na FCT, kwamishinan ‘yansanda don samun cikakken bayani game da garkuwar da kuma matakan da za a bi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din.
Wike ya bukaci shugabannin tsaro da suka samar da ‘yan sintiri a yankunan don su ke bibiyar ayyukan masu hakar ma’adinai, ya kara da cewa zai gana tare da takwaransa na ma’aikatar albarkatun kasa, Dele Alake, domin dakile hakar ma’adinai ta barauniyar hanya a birnin tarayya.
Kazalika, karamar ministan birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, da babban sakataren hukumar bunkasa shiyyar birnin tarayya FCTA, Mr Olusade Adesola, sun nuna kwarin guiwarsu kan hukumar kula da birnin tarayya Abuja.
Da yake magana kan matsalolin da yankin Kwari ke fuskanta, shugaban yankin, Danladi Chiya, ya roki ministan da karamin ministan birnin tarayyar da su zo domin taimaka musu.
“Tun lokacin da muka ji labarin nadinku, muka ji dadi da fatan cewa matsaloli za su zo karshe.”
“Babban matsalarmu da ke fuskantar dukkanin yankunan shida na Abuja shi ne matsalar tsaro. Ko a yau (Alhamis) mutum 19 aka yi garkuwa da su a yankin Bwari. Yanzu nake samun labarin cewa mutanen yankin sun fi kwanaki shida a hannun masu garkuwa.”