Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya nuna farin cikinsa game da hukuncin da Kotun Sauraron Korarrakin Zaben Shugaban Kasa (PEPC) ta yanke, wacce ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Gwamna Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga demokradiyya da gaskiya.
- Lalacewar Hanyar Bauchi Zuwa Gombe Ta Zama Tarkon Mutuwa Ga Matafiya – Gwamna Inuwa
- Jihar Gombe Ta Samu Nasarori Cikin Shekaru 26 Da Kafuwarta – Gwamna Inuwa
Inuwa ya ce wannan wata ‘Yar manuniya ce da ke tabbatar da amincewar al’ummar Nijeriya ga shugabancin shugaba Tinubu.
Gwamna Inuwa ya ce “Wannar nasara ta nuna irin karfin da demokradiyyarmu take da shi.”
Gwamnan ya bayyana hakan ta wata sanarwa da ta fito ta hannun daraktan yada labaransa, Ismaila Uba Misilli, inda Inuwa ya yaba da yadda kotun ta yi watsi da karar hadin gwiwa da jam’iyyun PDP da Labour da kuma PDM suka shigar, tare da ’yan takararsu na shugaban kasa, yana mai bayyana matakin a matsayin mai karfafa guiwa da ra’ayin jama’a da kuma nuna gaskiya ga tsarin zaben Nijeriya.
Gwamnan ya kuma taya jam’iyyar APC murna tare da jinjinawa tawagar lauyoyin da suka wakilci shugaban ƙasa da jam’iyyar.