Rundunar ‘yansandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa mutane biyar sun samu rauni daban-daban a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai karamar hukumar Gwoza da ke jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Abdu Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), a ranar Asabar a Maiduguri.
- Firaministan Sin Ya Bukaci A Karfafa Ci Gaba Da Kuma Daidaita Farashin Kayayyaki
- Zaben 2023: Atiku Ya Lashe Mazabar Shugaban Majalisar Dattawa A Yobe
Ya ce ‘yan ta’addan sun yi harbin bindiga da dama a kan masu kada kuri’a daga kololuwar tsaunin Mandara, inda ya ce mutane biyar sun samu raunuka a harin.
Umar ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da mata biyu da maza uku.
“Kokarin da sojoji suka yi a yankin ya taimaka wajen fatattakar ‘yan ta’adda, wanda ya tilasta musu tserewa,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce tun daga lokacin zaman lafiya ya kankama yayin da ake ci gaba da kada kuri’a yayin da wadanda abin ya shafa aka kai su asibiti.
A halin da ake ciki, Kungiyoyin Fararen Hula a Borno (NECSOB) ta bayyana kwarin guiwarta kan masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a jihar.
Shugaban kungiyar, Mista Bulama Abiso, wanda ya jagoranci tawagar masu sa ido a zaben, ya bayyana fitowar jama’a a matsayin abin karfafa gwiwa.
Sai dai ya lura cewa na’urar BVAS ta haifar da tsaikon fara kada kuri’a da wuri.
Abiso ya bukaci masu kada kuri’a da su rika gudanar da ayyukansu cikin tsari domin saukaka gudanar da zaben.