Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi ta kama mutum bakwai dangane da zargin fyaɗe da kuma mutuwar wata budurwa mai shekaru 18 a unguwar Fawari da ke ƙaramar hukumar Misau.
Cikin waɗanda aka kama har da Dallas Ayuba mai shekaru 21 da Usman Umar mai shekaru 22.
- Sin Da Kenya Sun Daukaka Dangantakarsu Yayin Da Xi Da Ruto Suka Gana
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Sin Da Birtaniya Da Su Kiyaye Tsarin Kasa Da Kasa Da Aka Kafa Bayan Yakin Duniya Na Biyu
‘Yansanda sun ce mutanen sun yi wa budurwar fyaɗe da yawa har ta kai ga ta samu ciki.
Daga baya, mutanen biyu sun biya wani ɗalibi mai suna Abubakar Muhammad mai shekaru 35 da ke makarantar AD Rufai College of Legal and Islamic Studies, kuɗi Naira 40,000 domin ya taimaka wajen zubar mata da cikin ta hanyar allura.
Bayan Abubakar ya yi mata allurar, sai budurwar ta faɗi ta suma.
An garzaya da ita asibitin Misau, daga nan aka mayar da ita zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, inda aka tabbatar da mutuwarta.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Ya ce waɗanda aka kama sun amsa laifin kuma sun bayyana sunayen wasu da suka haɗa kai da su.
Cikin sauran waɗanda aka kama har da Alkali Kawu, Maule Mai Ride, Mai Tumatir, Danguli, Yakubu da Kura.
Wakil ya ce bincike yana guduna a hedikwatar ‘yansanda ta Misau, kuma sun ƙudiri aniyar ganin adalci ya tabbata.
Ya ƙara da cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifin da suka aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp