• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutum 900 Kacal Aka Gano Cikin 15,000 Da Suka Bace A Arewa Maso Gabas – ICRC

by Khalid Idris Doya
2 years ago
ICRC

Kwamitin agaji ta ‘Red Cross’ na kasa da kasa (ICRC) ya bayyana cewar kusan fararen hula 900 ne kawai ana gano a shekarar 2022 daga cikin mutum 15,000 da aka bada rahoton bacewarsu sakamakon aikace-aikacen ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno da wasu sassan arewa maso gabas daga 2015 zuwa yanzu.

ICRC ta kara da cewa ta yi rijistan sama da mutum dubu 23,000 da suka bace a fadin Nijeriya sakamakon rikice-rikice.

  • Ba Za Mu Sake Lamuntar Kumbiya-kumbiyar Da Ake Tafkawa Wurin Fasfo Ba – Ministan Cikin Gida

Jagorar tawagar kariya da alaka da iyalai ta ICRC, Lillian Dube, ce ta shaida hakan a ranar Alhamis a bikin tunawa da mutanen da suka bace da ya gudana a Ngarannam, tsohowar sansanin ‘yan Boko Haram da ke Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

“A shekarar 2022, ICRC ta samu nasarar gano mutum 900 da suka bace tare da maidasu ga iyalansu.

“ICRC na shirya taron tunawa da wadanda suka bace ne domin nuna goyon baya ga iyalan mutanen da suka bace. Mun yi rijistan mutanen da suka bace su 15,000 a jihar Borno da jihohin da suke arewa maso gabas. Zai kuma iya kasancewa akwai wasu mutane da yawan gaske da su ma sun bace amma ba a samu shigar da su cikin rijista ba. Mutane da yawa a cikinsu an rabasu da iyalansu ne a 2015,” Dube ta shaida.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Shi kuma jami’in kiwon lafiyar kwakwalwa na ofishin ICRC a Maiduguri, Ahmed Kyari, ya ce, an ware ranar 30 ga watan Agustan 2023 domin tunawa da wadanda suka bace a rikice-rikice, ya kara da cewa, ta’addancin ‘yan Boko Haram ya shafi mutane da daman gaske a Borno.

Shi kuma a nasa jawabin, jagoran tawagar ICRC a Maiduguri, Mr Serge Zogg, ya mika sakon alhinunsu ga mutanen da aka raba da ‘yan uwa na tsawon lokaci.

Ta ce, ICRC ta kasance mai taimakon jama’a da agaji domin kare rayuka da mutuncin wadanda hare-hare ke shafa tare da sanar musu da tallafin da suke bukata.

Shettima Mohammed, wanda ya rasa ‘yar uwansa shekara 11 da suka wuce a rikicin Boko Haram, ya ce, har yanzu wannan rashin na sanya shi cikin dimuwa, ya ce, duk lokaci da aka bude kofar gidansa, gani yake kamar ‘yar uwansa ce ta dawo.

Ita ma Fatima Bunu Malik, da ta rasa kawunta a rikicin Boko Haram shekaru takwas da suka wuce a karamar hukumar Kukawa, ta misalta cewa matar kawun nata ta shiga matukar rashin hankali wacce ta rasu kwanakin baya, yanzu haka ‘ya’yansu guda uku duk sun zama marayu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
Manyan Labarai

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya
Labarai

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Next Post
Xi

Xi Ya Yabawa Abotar Sin Da Amurka A Cikin Amsar Wasika Zuwa Ga Jikan Janar Joseph Stilwell

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.