Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci 15 inda ya ba su umarnin wadata mutane da takardun Naira 200.
A cewarsa, ya tattauna da su yadda za a sassauta karancin kudi da ake fama da shi a kasar nan, biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar a safiyar ranar Alhamis.
- NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar Watan Nuwamban 2022
- ‘Yan Jihar Bauchi Sun Yabawa Buhari Kan Amincewa Da Ci Gaba Da Amfani Da Tsohuwar 200
Buhari ya ba da umarnin a sake dawo da tsoffin takardun kudi na N200 don ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 10 ga Afrilu.
Emefiele ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan halartar taron da Buhari ya yi da kwamitin majalisar wakilai a fadar shugaban kasa inda sabon tsarin musanya naira.
Emefiele ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a samar da tsofaffin takardun kudi na N200 nan take.
A safiyar ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin duk da umarnin da kotun koli ta bayar.