A ranar Talata 8 ga watan Afrilu 2025 ne aka gudanar da babban taron kamfanin jaridar LEADERSHIP da ke Abuja, inda ake karrama ‘yan Nijeriya da suka yi fice a fannoni daban-daban na bunkasa rayuwar al’umma. Cikin wadanda aka karrama akwai Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, inda kamfani ta bashi lambar yabo a kan jajircewarsa wajen bunkasa harkokin ilimi a fadin jihar.
A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Gwamna Abba ya bayyana cewa, yana matukar muhimmantar da wannan karramarwar da LEADERSHIP ta yi masa, musamman ganin cewa, ita da kanta ta tattara dalilai da hujjojin da suka gamsar da ita “Har ta ga ya dace ta karrama ni, ba tare na nema ba ko kuma na yi musu wani hasafi ko kamun kafa” in ji shi.
- Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni
- Yadda Bankin Stanbic IBTC Ke Bunkasa Tattalin Arzikin Abokan Huldarsa
Ya ce, ya sadaukar da karramawar da aka yi mishi ga dukkan ‘yan Nijeriya marasa karfi a duk inda suke. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan bunkasa rayuwar yara ta hanyar samar musu da yanayin da za su samu ilimi domin inganta rayuwarsu.
Ya ce, mun samar wa daliban makarantu yunifam, da motoci domin saukaka wa dalibai zirga-zirga tsakanin makarantu da gidajensu. “Akan haka mun kara yawan kasafin kudin bangaren ilimi a wannan shekarar zuwa kashi 31, saboda sanin muhimmancin ilimin matasa ga bunkasar jiharmu” in ji shi.
Taron ya samu halartar kwamishinoni da manyan ma’aikatan gwamnatin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp