Hamshaƙin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya fi fifita kishin ƙasa a kan samun riba kawai cikin harkokinsa na kasuwanci inda hakan ya sa ya fi mayar da hankali a kan kafa kamfanoni a Nijeriya har ma da Afirka baki xaya domin nahiyar ta zama mai dogaro da kanta.
Attajirin wanda yake bayani ga manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai da ya karɓi baƙuncinsu a sabuwar matatarsa ta mai da ke yankin Lekki na Legas, ya ƙara da cewa, matuqar qasashenmu na Afirka ba su mayar da hankali a kan samar da kamfanonin da za su riƙa sarrafa abubuwa na buƙatun al’ummominsu a cikin gida ba, tabbas, za su ci gaba da fitar da ayyukan yi zuwa kasashen duniya, su kuma suna caka wa kansu wuka ta hanyar shigo da karin talauci cikin kasashensu.
- Har Yanzu A Gidan Haya Nake Zaune A Abuja – Aliko Dangote
- Har Yanzu Kamfanonin Mai Na Kasashen Waje Na Mana Kafar Ungulu Wajen Samun Danyen Man Nijeriya – Dangote
Kamar yadda ya yi bayani, daga irin wannan kishin ne, ya samar da matatar mai da za ta rika tace danyen mai ganga 650,000 a kullum da zai wadaci Nijeriya da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.
Ya ba da tabbacin cewa a karshen wannan watan da muke ciki, man fetur da matatarsa take tacewa zai shiga kasuwa a Nijeriya.
“Ka san wahalar fetur ana yin ta idan ka duba tarihi tun lokacin Gowon, a 1972, ba a samun mai ya wadata. To amma idan Allah ya yarda, idan muka soma (fitar da mai), Nijeriya ba za ta iya shan fiye da rabin abin da za mu yi ba… In sha Allahu daga wannan watan (Yuli) za mu soma (fitarwa).” A cewar Dangote lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa.
Dangote wanda kamfanoninsa ke zaman rukuni daya tilo mafi samar da ayyukan yi a Nijeriya mai ma’aikata fiye da 100,000, ya bayyana cewa ya himmatu wajen ganin an bukasa harkokin noma a Nijeriya inda yanzu haka ya mayar da hankali a kan noman shinkafa, da rake da kuma tumatir tare da kakkafa masana’antun sarrafa su.
“Mun samar da kamfanin sarrafa tumatir a Kano, za mu bai wa manoma kudi su yi noma kuma ba tare da fargabar rashin samun kasuwar sayar da amfanin gonarsu ba, mu za mu saya, kuma idan sun ga farashin da za mu saya ya yi kadan, za su iya kaiwa inda suke so su sayar… a Nijeriya, kasarmu ta noma da ake nomawa ba ta fi kashi 8 cikin 100 kacal ba.” Ya bayyana.
Bugu da kari, Alhaji Dangote ya nunar da cewa, kamfaninsa na taki ya dakatar da sayarwa a kasashen waje saboda yadda ake bukatar takin a gida a halin yanzu.
“A kamfanin takinmu muna da taki na Urea wanda ba samfurin NPK ba, da ya fi karfin abin da Nijeriya ke nema. Kashi 20 cikin 100 ne kawai Nijeriya za ta iya dauka, amma ragowar na kaiwa kasar waje ne mu sayar. Amma kowane irin taki ne in dai Urea ne ake nema muna da shi kuma muna sayarwa, amma a yanzu haka ma ba ma fitarwa waje duka muna sayarwa a cikin gida saboda yanzu (damina) lokacin neman taki ne… Idan muna da gas, za mu iya yin takin har tan miliyan uku, to amma gaba dayan kasuwar nan (Nijeriya) ba ta ma kai tan miliyan daya ba na Urea.” In ji shi.
Har ila yau, zauren tattaunawar Attajirin da shugabannin kafafen yada labarai ya dau jinjina yayin da aka ji yana bayyana cewa ba shi da gida a Amurka ko Landan, sannan hatta gidan da yake sauka a Abuja na haya ne ba na kashin kansa ba.
Ya ce sha’awarsa ga ci gaban masana’antu a Nijeriya shi ne kadai dalilin da ya sa ya yanke shawarar kin mallakar gidaje a kasashen waje.
Dangote ya bayyana cewa ya taba samun gida a Landan, amma ya sayar da shi a shekarar 1996.
“Ba ni da gida a Landan ko Amurka saboda ina so in mayar da hankali kan bunkasa masana’antu a Nijeriya. Na dauka cewa idan ina da wadannan gidajen, ana iya samun wani dalili da zai dauke hankalina zuwa zama a can.
“Ina matukar sha’awar ganin ci gaban Nijeriya kuma ban da gidana na Legas, ina da wani a jihata ta asali Kano da kuma na haya a Abuja.” In ji shi.
A jawabinta na rufewa, Babbar Daraktar Harkokin Kasuwanci na Kamfanonin Dangote, Fatima Dangote, ta yaba wa mahaifin nasu a kan yadda yake nuna kishin kasa karara cikin harkokinsa na kasuwanci.
Ta kara da cewa, “Ban taba ganin wanda ya kai mahaifina aiki tukuru ba, wani lokaci ina mamakin yadda ba ya jin kasala a jikinsa. Sannan duk kamfanin da zai kafa abin da yake fara dubawa shi ne kishin kasa ba riba ba, domin akwai abubuwan da zai iya yi da yawa kamar zuba kudi a kamfanoni irin na su Elon Musk ko na Microsoft da zai samu riba mai yawa, amma bai yi hakan ba, yana duba kishin ci gaban kasa ne da nahiyarmu. Da ma a ce mun sami karin jajirtattun mutane kamar mahaifina a Nijeriya, kasar za ta fi samun ci gaba.” Ta bayyana.
A yayin ziyarar dai, an kewaya da shugabannin kafafen yada labarun sassa daban-daban na katafariyar matatar ta Dangote wacce ita ce ta farko da ta hada manyan sassan matatar mai a wuri daya a duk fadin duniya da aka zuba jarin fiye da Dala biliyan 20.
Bugu da kari, daga cikin abubuwan birgewa da aka gani a matatar akwai matasa ‘yan Nijeriya masu jini a jika da aka dauke su aiki a sassa daban-daban ciki har da wani dakin gwaje-gwaje na musamman da aka cika da na’urorin tantance ingancin mai na zamani irinsu na farko a duk fadin Afirka.
Matatar Man Dangote dai tana kunshe da manyan rumbunan adana mai masu cin miliyoyin lita akalla 177, da wuraren lodi akalla 86 wadda za su iya yi wa tankokin mai 2500 lodi kullum, sannan za ta iya samar da karfin wutar lantarki megawat 435 domin amfanin kanta da kuma rabawa ga jihohi makota.
Daga cikin rukunin kamfanonin na Dangote dai akwai na Siminti a kasashe 10 da yake samar da tan miliyan 52 na siminti, sai na abinci da yake samar da sukari da gishiri da kuma karamar taliya baya ga matatar man da kuma sashen sana’ar kayan gona.
Kudin Da Kamfaninsa Zai Samu Dala Biliyan 30 Zai Farfado Da Darajar Naira, In Ji Shi
A halin da ake ciki kuma, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote; ya bayyana cewa, kudirin kamfaninsa shi ne; zama kan gaba wajen samar da kudaden waje a kasuwar hada-hadar canji nan ba da jimawa ba, yayin da yake tsammanin samun kudaden shiga kimanin dala biliyan 30 daga nan zuwa shekarar 2025.
A ziyarar da ya kai matatar man fetur na Dangote da kamfanin takin zamani da samar da sinadarai tare da shugabannin kafafen yada labarai a karshen makon da ya gabata, ya ce babban burinsa shi ne ya zama mai cin gashin kansa ba tare da dogaro da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ba waje samun da kudaden musaya, kana ya shaida cewa za su rage kasuwancinsu na siminti daga kashi 75 zuwa kashi 15 cikin dari a nan gaba kadan.
Abin da ake sa ran samu na kudaden waje ta hanyar kasuwancin nasa; zai farfado da darajar Naira tare da kara mata tagomashi a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya.
A cewar Dangoten, matatar ta fara aiki ne a wannan shekara ta 2024, inda a farko ta fi mayar da hankali a kan tace wasu sinadarai na masana’antu, dizal, man jirgin sama da sauransu.
Bugu da kari, ya yi hasashen matatar za ta rika tace gangar mai 500,000 a kowace rana tare da samun danyen mai daga jiragen ruwa 15 a kowane wata har zuwa watan Agusta, kana ana sa ran adadin gangar da ake tacewa ya karu 550,000 a kowace rana zuwa karshen shekarar nan, daga bisani kuma idan Allah ya kai mu watanni uku na farkon badi, adadin zai karu zuwa ganga 650,000 a kowace rana.
“Za a fara samar da man fetur a watan Yuli tare da fara sayarwa a watan Agusta,” in ji Dangoten.
Dangoten ya kuma yi nuni da cewa, kamfanin nasa yana da niyyar sanya matatar mai da kamfanin takin zamani da na samar da sinadarai a kasuwar shinku a farkon sulisin shekarar 2025. Inda ya ce, hakan zai bai wa ‘yan Nijeriya damar shiga cikin jerin masu mallakar wadannan kamfanonin.
“Saboda yanayin irin kasuwancinmu, muna da burin shigar da matatar man fetur da kuma kamfanin takin zamani kasuwar hannayen jari daga nan zuwa karshen shekara. Ko ma dai yaya ake ciki, muna sa ran shigar da su kafin karshen farkon sulisin shekara mai zuwa. Ko shakka babu, wannan zai ba mu damar sayar da hannun jari; domin ‘yan Nijeriya su ma su shigo a dama da su,” in ji Dangoten.
Ita dai matatar man ta Dangote; za ta rika sarrafa ganga 650,000 a kowace rana a matsayin matatar man fetur mafi girma a duk fadin Afirka, sannan kuma ita kadai ce mai irin wannan girman da ta hade dukkan sassanta a wuri daya, inda shi kuma kamfanin takin Dangote ya zama mafi girma a duk fadin Afirka, yayin da shi kuma na simintin Dangote ya kasance mafi karfin jari a Nijeriya.
Alhaji Aliko ya kuma bayyana cewa, rumbunan adana mai na matatarsa na daukar kimanin lita biliyan 4.5, wanda za su iya daukar danyen man da Nijeriya ke bukata na tsawon kwana 20 tare da adana kwatankwacin man da Nijeriya za ta yi amfani da shi na tsawon kwanaki 15, sannan ya jaddada cewa; matatar za ta rika samar da lita miliyan 53 na fetur a kowace rana tare da samar da tan miliyan 1.1 shi ma a kowace rana.
Kazalika, matatar ta kunshi manya-manyan wuraren lodin man da ta tace 86, tare kuma da wasu na’urorin na sauke danyen mai daga teku. Bugu da kari, matatar ta kuma kunshi sashen sarrafa sinadarin ‘polypropylene’ kiloton 900 wadda za ta iya samar da tan 36,000 a kowace shekara na ‘sulphur’ da kuma tan 585,000 na ‘carbon black’ a kowace shekara.
Dangote ya ce, a cikin shekaru 40 da suka gabata; hada-hadar kasuwancin rukunin kamfanoninsa sun bunkasa sosai, daga kasuwancin kayayyakin masarufi zuwa na rukunan kamfanoni daban-daban. Ya jaddada cewa, wannan sauyi ya samo asali ne daga babban burin da yake da shi na ganin Nijeriya ta iya wadatar da kanta a sassa daban-daban domin samun habakar tattalin arziki.
Ya yi nuni da cewa, rukunin kamfanonin wanda ya fara a matsayin kamfanin saye da sayarwa a shekarar 1978, ya habaka ta hanyar zuba jari a harkokin siminti, noma, takin zamani, man fetur, gas, motoci, ababen more rayuwa da sauransu.
Ya ci gaba da cewa, rukunin kamfanonin yana gudanar da harkokinsa ne bisa yakinin cewa makomar Afirka ta dogara ce a kan yadda za ta iya sarrafa albarkatunta da kanta da iya yi wa kanta abubuwan da take bukata. Dangote, ya kuma jaddada cewa, nahiyar na shigo wa kanta da fatara ce da fitar da ayyukan yi zuwa kasashen waje ta hanyar fitar da albarkatunta da kuma shigo da kayan da aka sarrafa a waje kasashen waje.
A nashi bangaren, Mataimakin Shugaban Kamfanin Man Fetur na Dangote, Debakumar Edwin; ya sake nanata kudirin kamfanin na inganta masana’antun cikin gida da sauran sassa masu muhimmanci na tattalin arziki.
Ya ce, kamfanin Dangote ya bai wa matasa ‘yan Nijeriya damar gudanadar da muhimman ayyuka a kamfanoninsa, inda da dama daga cikinsu suka zama kwararru a wasu kasashen ketare.
Edwin ya jaddada matsayin matatar a matsayin matatar da ta hade sassanta wuri daya mafi girma a duniya da wacce kamfanin cikin gida Nijeriya shi kadai ya yi aikin gina ta, yana mai nuni da irin gagarumin ci gaban da aka samu a bangaren aikin injiniya da na gine-gine.
Ya kara da cewa, galibin matatun man da ake da su kamfanonin kasashen waje ne suka gina, don haka abin alfahari ne a samu wani kamfani na gida Nijeriya da zai iya kwangilar aikin injiniya, shigo da kayayyakin da ake bukata na aikin da gine-gine kai tsaye kuma a lokaci guda, ya zana tare da gina katafariyar matatar mai mai kunshe da sassanta a wuri guda. Ya ce, hakan ya kara wa ‘yan Nijeriya da dama; musamman masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa a harkar da kuma amannar cewa an samu wani kamfanin Nijeriya da zai iya gina matatar mai a ko’ina a fadin duniya.
“Babban abin alfahari ne a ce, matata mafi girma a duniya mai kunshe da sassanta a wuri guda an samu wani kamfanin gida Nijeriya da ya iya kwangilar zanawa da gudanar da aikin injiniya da gine-gine a lokaci guda da kashi dari bisa dari.” In ji shi.
Yayin da take mika godiyarta ga Shugabannin Kafafen Yada Labarai, babbar daraktar kula harkokin kasuwanci ta rukunin kamfanonin Dangote, Fatima Dangote; ta nanata kudirin rukunin kamfanonin na kara kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasa. Haka nan, ta yaba da jajircewar Aliko Dangote wajen ciyar da Nahiyar Afirka gaba.
“Shi (Dangote), ya himmatu wajen tabbatar da nasarar Nijeriya da Afirka a matsayin kasa da nahiya, ba kawai mun mayar da hankali ba ne a kan riba don magance matsaloli tare da cimma bukatunmu a dukkanin masana’antunmu na Afirka ba. Sannan, ta hanyar tabbatar da ingancin kayayyakin da ake bukata a duniya; mun sha damarar fitar da kayayyakinmu zuwa kowace nahiya a duniya”, in ji ta.
Haka zalika, Fatima ta yi nuni da cewa; rukunin kamfanonin Dangote ba kawai shi ne kamfani mafi samar da ayyukan yi ba, amma yana sahun gaba a cikin manyan kamfanonin da suke biyan haraji a kasar nan duk shekara tare da bin daukacin dokokin harajin da suka dace.
“Mun shahara a matsayin guda daga cikin manyan kamfanoni masu samar da aikin yi. Sai dai kuma, ba wannan ne ba kawai, muna tabbatar da ganin ma’aikatanmu na cikin jin dadin rayuwa da kuma nishadi a koyaushe. Mununiya a kan haka ita ce shigar mu cikin jerin kamfanoni mafi biyan albashi mai tsoka a kasar nan. Tasirin da muke yi a bangaren samar da ayyukan yi; ya kai ga samar da dubbannin ayyuka yi a tsakanin al’ummomin da muka kafa masana’antunmu a yankunansu”, in ji ta