Gwamnan Jihar Kaduna mai barin gado, Nasir Ahmed El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai zama shugaban ma’aikatan fadar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahme Tinuba, bayan kammala wa’adin mulkinsa a matsayin gwamna a ranar 29 ga Mayu.
Da yake maida martani kan wasu rahotonnin da ke cewa da yiwuwar ya zama shugaban ma’aikatan sakamakon irin kusancin da yake da shi da Tinubu a lokacin yakin neman zabe, gwamnan ya ce, a maimakon hakan, ya gwammace ya ya koma bangaren kamfanoni masu zaman kansu domin ya ci gaba da ba da gudunmawa wajen bunkasa ci gaban kasa.
An dai yi ta yada labarai daban-daban da ke nuni da cewa da El-Rufai zai iya kasancewa shugaban ma’aikatan fadar zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai an jiyo gwamnan kamar yadda Daily Post ta nakalto yana fada a wajen kaddamar da aiki a jihar Gombe jiya, “Zan bar ofis nan da kwana 22, zan kasance mai ba da shawara a gefe a duk lokacin da kuke bukata ta.
“Zan kasance a bangaren kamfanonin masu zaman kansu, ba wata kujerar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba (CoS).” In ji El-Rufai.