Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce ya kalubalanci nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Obi, ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, inda ya yi ikirarin cewa ba yana kalubalantar “sakamakon” zaben.
- Da Dumi-Dumi: CBN Ya Amince Da Ci Gaba Da Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira
- Ban Taba Ba Ministan Shari’a Da CBN Umarnin Su Ki Mutunta Umarnin Kotun Koli Ba – Buhari
Tsohon Gwamnan Anambra ya dage cewa yana so ya tsaya takara a tsarin da INEC ta ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.
“Bayan amsar tambayar da na yi a lokacin da na bayyana a gidan talabijin na Arise a safiyar yau, ina so na bayyana cewa a kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa (PET), ina kalubalantar tsarin zaben INEC da ya kai ga ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa,” Obi ya wallafa a shafinsa na Twitter.
An ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 1 ga watan Maris.
Tuni Obi ya garzaya kotu, bisa zargin tafka kura-kurai da hukumar zabe ta yi.
Saboda haka, Kotun Daukaka Kara ta ba da izinin duba duk wasu muhimman kayan da aka yi amfani da su don zabe.