Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya kwana a garin Marte ne domin ƙarfafa gwiwar mazauna garin bayan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai makon jiya.
Zulum ya ce fiye da mutane 20,000 ne suka tsere daga garin domin tsira da rayukansu, amma gwamnati ba za ta bari Boko Haram su karɓe garin ba.
- Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna
- Gwamna Bala Ya Yi Alhinin Rasuwar Yariman Bauchi, Garba Muhammad Sambo
Ya bayyana cewa aƙalla garuruwa 300 ne suka fuskanci barazanar ta’addanci a yankin, kuma gwamnati na ɗaukar matakan tsaro tare da haɗin gwiwar sojoji, ’yansanda da kuma ’yan sa-kai da aka horas domin kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Gwamnan ya buƙaci taimakon Gwamnatin Tarayya saboda yadda hare-haren suka tsananta, musamman a kwanakin baya.
A makon da ya gabata kaɗai, Boko Haram sun kai hare-hare sau shida a sassa daban-daban na Jihar Borno, wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi na sojoji da fararen hula.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp