ZARAH MUHAMMAD SUNUSI wacce aka fi sani da UMMU HEEBBAT, daya ce daga cikin marubutan littafi hausa na yanar gizo, ta kuma bayyana wa masu karatu irin gwagwarmayar da ta sha bayan fara rubutunta har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanki.
Sunana Zara Muhammad Sunusi wacce aka fi sani da Ummu Heebbat.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Tarihina shi ne an haife ni a 1998 a garin Gaidam dake Jihar Yobe. Na yi firamare sakandare, NCE duk garin Yobe, sannan inada aure har da yara biyar a yanzu haka.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar rubuce-rubuce?
Yawan karatun littafai da kuma son na bayar da gudummawa kamar yadda littafi ya bani gudummawa a cikin rayuwata sandin yawan karanta su.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Eh! to na fara rubutu da himma, a tunanina abin da sauki saboda yadda nake jin cewa ina da labarai masu yawa wanda kuma zan iya rubuta su. Sai dai kash! Ashe ba nan gizo ya ke sakar ba, domin kuwa ban iya komai na ka’idojin rubutu ba, kuma ban taba tsammanin cewa sai da su labari yake ma’ana ba. To a nan ne na sha gwagwarmaya wajen koyo wanda har yanzu akai na ke.
Ko akwai wani kalubale da ki ka fusknta wajen iyayenki ko mijinki lokacin da za ki fara rubutu?
Gaskiya ban fuskanci komai ba sai dai irin raha da wasa da dariya da tsokana da dangina suke yi min a lokacin na cewa; zan zama mai shirya karya, wannan kalmar na fara kokarik fahimtar da su asalin waye marubucin kuma suka amince suka saka min albarka .
Za ki kamar shekara nawa da fara rubutu?
Na fara rubutu a shekarar dubu biyu da ashirin da daya.
2021.
Kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Na rubuta labarai dogaye guda shida gajere guda hudu.
Ya farkon farawar ya kasance?
Na fara cikin sauki kasancewar na samu malamai maza da mata wanda suka taimaka mun da hanyoyin farawar sa kuma shawarwari.
Kamar wane bangare ki ka fi maida hankali akai wajen yin rubutu?
Gaskiya na fi rubuta labari a kan lamari na zamantakewar ma’aurata kusan duka labarai na a kan haka suka tafi sai kalilan ne da suka karkata.
Wane labari ne ya fi baki wuya cikin labaran da ki ka rubuta?
Eh! to, littafin da ya fi bani wahala wurin rubuta shi shi ne littafin SANIN GAIBU. Dalilin da ya sa na sha wahala kuwa shi ne, a lokacin da aka tambaye ni cikin gaggawa saboda labarin na gasa ne amma kuma dogon labari ne na tsawon wata guda, ya sunan labarin nawa za a yi list ban shirya komai ba, ban ma san wane suna zan saka ba, kawai sai sanin gaibu ya fado min cikin zuciyata, sai na bayar da wannan sunan to na sha wahala kafin na saka labari mai wannan taken. Bayan haka ina cikin rubutun wayata ta samu matsala tsawon mako guda kafin na yi wata.
Kin taba buga littafi?
Eh! na buga guda daya sunan sa WATA RAYUWA.
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhmdulillah na samu nasara wadanda nake farin ciki da su idan na tuna, kamar; shi littafin sanin gaibu da na baki labari ni ce na zo ta hudu a gasar da muka yi a bidden wani group na marubuta. Sannan ina alfahari da nasarar saboda shi ne karan farko dana fara nasara. Kuma kamar shi littafin wata rayuwa tun kafin na gama shi na samu mai siya wacce ta siya da mutuwar daraja ma kuwa. Sannan irin addu’o’in dana samu a lokacin da nake rubuta littafi bayan gangami gaskiya ba zan mance da su ba.
Wane irin kalubale ki ka taba fuskanta game da rubutu?
Gaskiya ban taba samun wani kalubale a rubutu ba wanda ya wuce wahalr da nake sha wajen hada kalma da rabawa ba.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Burina a rubutu shi ne yau a ce na bude idanuna na ga na gama sanin dukkan wasu ka’idojin rubutu musamman wajen hada kalmar da take a rabe da kuma rabe wacce ta ke a hade.
Ko akwai wanda ya taba bata miki rai game da rubutu?
Gaskiya ba wanda ya taba batamin rai game da rubtuna sai dai yabawa ma sha Allah na gode Allah.
Wane abu ne ya ke saka ki farin ciki da zarar kin tuna shi?
Ina jin dadi da farin ciki idan na tuna yau burina ya cika na amsa sunan marubuciya kuma ina rubutun da ke kama zuciyar al’umma da suke tare da ni.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu da matukar mahimmanci a rayuwata gaskiya, saboda haka ko sunan marubuci na ji sai na waiwaya domin ji nake na samu ‘yan uwa kuma ina kaunarsa sosai rubutun a zuciyata.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Eh! Ina sana’a.
Kamar wace irin sana’a kuma ya ki ke iya hada sana’arki da rubutunki?
Kowanne ina bashi lokacinsa ne, duk abin da mutum zai yi idan ya shirya masa ko kuma ya ware wa kowanne lokacinsa to ya huta, kuma abin zai zo masa da sauki.
Kamar wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Bayan Asuba da kuma lokacin da nake cikin damuwa ina kaunar rubutu sosai a wannan lokacin, da zarar raina ya baci to zan ji ina bukatar nayi rubutu.
Me za ki ce da masu karanta labaranki?
Ina matukar alfahari da su, ina kuma yi musu fatan alheri a dukkan inda suke a rayuwa.
Allah ya amsa mana ibadun mu na wannan wata mai dumbin daraja da muke ciki da ni da su da sauran al’umma gaba daya.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Gaisuwa ta musamman ga kawata Ummu Ramalat da ke zaune a garin Maiduguri, gaisuwa ta musamman ga Aunty na Hajja da ke zaune a Jihar Yobe a garin Gaidam, gaisuwa ta musamman ga kawata Sajida Fadima Kaduna, gaisuwa ta musamman ga Aunty na Hadiza Dm Auta, gaisuwa ta musamman ga kawata Jamila ‘Yar Malam.
Muna godiya
Ni ma.na gode.