Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya bayyana rashin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi na ƙasa da kuma na rashin ɗan kashin ƙasa, yana mai cewa ya rasa abokin aiki, dattijo mai daraja.
A cikin saƙon ta’aziyya da ya fitar ranar Lahadi, Jonathan ya bayyana alhini kan rasuwar shugaban da ya gaje shi a mulki, wanda ya rasu yana da shekaru 82.
- Rasuwar Buhari: Nahiyar Afirka Ta Yi Babban Rashi — Kungiyar Gwamnoni Ta Nijeriya
- Rasuwar Buhari: An Yi Rashin Ɗan Ƙasa Na Gari, Abin Koyi — Kungiyar Gwamnonin Arewa
Jonathan ya yabawa Buhari a matsayin ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, shugaba mai tsari da dattako, wanda ya yi wa Nijeriya hidima bisa gaskiya da rikon amana.
“Cikin alhini da raunin zuciya mai cike da jimami na samu labarin wannan rashi mai girma a ƙasa, na rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari,” inji Jonathan. “Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin manyanta, ni kuma na rasa aboki, dattijo mai daraja.”
Jonathan ya jaddada irin gudunmawar Buhari a matsayinsa na shugaban soja, kuma shugaban da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya.
Ya ce za a ci gaba da tunawa da Buhari a matsayin “shugaba mai jarumta, soja mai tsari kuma jami’in gwamnati mai sadaukarwa wanda ya ba da gudunmawa a ɓangaren samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.”
Ya kuma yaba da yadda rayuwar Buhari ta cika da ɗabi’un da suka ja hankalin ‘yan Nijeriya daga kowane ɓangare na rayuwa.
“A matsayinsa na shugaba, ya nuna tsantsar sadaukarwa da kishin ƙasa,” cewar Jonathan.
A ƙarshe, ya miƙa ta’aziyyarsa da ta iyalinsa a madadin gidauniyar Goodluck Jonathan zuwa ga iyalan Buhari da al’ummar jihar Katsina, da kuma dukkan ‘yan Nijeriya.
“Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus,” cewar Jonathan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp