Barista Batulu Muhammad Koguna ta bayyana kwarin gwiwar da lauyoyi mata suka samu a Jihar Kano, bisa nada Barista Dije Aboki a matsayin babbar mai shari’a ta jihar Kano.
Ta ce daukacin lauyoyi matan Jihar Kano da ma Nijeriya baki daya sun sami kwarin gwiwa, domin kuwa ya nuna cewa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da ma’aikatar shari’a da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shari’a sun amincewa da ita a matsayin babbar mai shari’a sakamakon cancanci ta.
- …Ya Kashe Uwargidan Da Yake Yi Wa Hidima Da Mahaifiyarta Gami Da Tafka Sata
- Uwargidan Gwamnan Kebbi Ta Tallafawa Mata 500 Da Buhunan Gyada Da Tsabar Kudi
Barista Batulu ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wani taro na karfafa gwiwar mata da ya gabata a Jihar Kano, wanda dimbin jama’a suka tofa albarkacin bakinsu.
Ta ce a matsayinta na lauya mace ta san Dije Aboki mace ce mai jajircewa da aiki tukuru da hakuri da kuma tsayawa kan gaskiya, don haka wannan mukami da aka ba ta ya dace da ita, sannan ba za ta ba matan Kano da al’umma Kano kunya ba.
Ta yaba wa kwamishinan shari’a na Kano da sauran lauyoyi maza da mata da masu ruwa da tsaki wajen nada Dije Aboki a matsayin babbar mai shari’a ta Kano.