Rundunar Sojin Sama ta ƙasa (NAF) ta kai wani hari na sama kan ma’ajiyar kayayyaki da matattarar ƴan ta’adda a Dabar Masara, yankin Kudancin Tumbuns na ƙaramar hukumar Monguno, Jihar Borno, inda ta hallaka da dama daga cikinsu tare da lalata muhimman motocin aiki.
An kai harin ne a ranar Lahadi, 14 ga Disamba 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wurin ana horar wa da samar da kayan aiki ga ƴan ta’adda.
- NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa
- Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
Bincike kafin harin ya gano motocin ƴan ta’adda da aka ɓoye ƙarƙashin ciyayi da kuma yawan motsin makamai, lamarin da ya tabbatar da cewa wurin cibiyar kayayyaki ce. A ranar harin, an sake tabbatar da waɗannan bayanai kafin a kai farmaki bisa ƙa’idojin aiki.
Bayan harin, rahoton tantance ɓarnar ya tabbatar da lalata motocin da kuma kashe ƴan ta’adda da dama. NAF ta jaddada cewa wannan nasara na nuna jajircewarta wajen amfani da bayanan sirri da hare-haren da suka dace domin murƙushe cibiyoyin ƴan ta’adda da ƙara tsaro a Arewa maso Gabas.














