ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa

by Zubairu M Lawal
9 months ago
NAFDAC

Hukumar NAFDAC ta lalata kayayyaki marasa inganci da kuɗinsu ya haura naira biliyan 5 a wani babban taron da aka gudanar a wurin zubar da shara na Angwan Rere da ke Lafia. Kayayyakin sun fito ne daga jihohin Nasarawa, Benue, da Kogi, da Neja da Filato, inda hukumar ta ce an cafke su ne sakamakon sintirin da ma’aikatanta ke yi domin daƙile yaɗuwar jabun kaya a kasuwanni.

Daraktar-Janar ta NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, wadda Daraktan Yankin Arewa ta Tsakiya, Kenneth Azikiwe, ya wakilta, ta bayyana cewa kayayyakin da aka lalata sun haɗa da abincin gwangwani marasa inganci, da kayan ƙara dandano, da magunguna na bogi, da kayan kwalliya marasa inganci, da sabulai na jabu, da sinadarai da sauran na’urorin lafiya da suka sabawa ƙa’ida. Ta ce wasu ‘yan kasuwa masu gaskiya su ne suka miƙa wasu daga cikin kayayyakin bayan sun fahimci hatsarin da suke haifarwa.

  • Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
  • EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja

NAFDAC ta jaddada cewa manufarta ita ce kare lafiyar jama’a ta hanyar kiyaye kasuwa daga shigar jabun kaya da marasa inganci. Farfesa Adeyeye ta ce hukumar za ta ci gaba da sintiri don tabbatar da cewa ingantattun kayayyaki kaɗai ake sayarwa. Ta kuma nemi jama’a da su ci gaba da ba da bayanai kan duk masu kerawa ko yada kayayyaki da ka iya cutarwa.

ADVERTISEMENT

NAFDAC

A nasa ɓangare, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Nasarawa, Usman Baba, wanda ya wakilci gwamnatin jihar, ya yaba wa NAFDAC bisa yadda take kare jama’a daga barazanar jabun kaya. Ya tabbatar da cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da ba da goyon bayan da ake bukata domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma da ingancin kayayyakin da ake amfani da su.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

NAFDAC
Zubairu M Lawal
+ postsBio
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    2027: Miyetti Allah Ta Yi Barazanar Ƙauracewa APC Kan Ci Gaba da Tsare Boɗejo
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Samar Da Abinci Mai Gina Jiki: Gwamna Sule Ya Duba Gonakin Shinkafa A Jangwa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda Ya Tallafawa Manoma Da Kayan Aikin Gona Na Miliyoyin Naira A Nasarawa

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
NAFDAC
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
NAFDAC
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce

Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
NAFDAC

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
NAFDAC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.