A Wasu jerin hare-hare da jiragen yakin sojojin saman Nojeriya suka kai, sun kashe dakarun kungiyar ISWAP 24 da ke samun horon yadda ake sarrafa bama-bamai a yankin tafkin Chadi.
An kai harin ne a ranar Lahadi a Tumbun Hamma, daya daga cikin sansanonin da aka gano ana baiwa ‘yan kungiyar horo a tafkin Chadi.
A cewar wata majiya mai karfi, ‘yan ta’addan suna samun horon sarrafa makamai da bama-bamai ne a wurin na tsawon kwanaki shida a jere.
A wani labarin kuma, wani jirgin saman NAF da ke karkashin rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai (OPHK) ya kai wasu hare-hare a wuraren da ‘yan ta’adda suke a Tumbun da ke kusa da tafkin Chadi.