Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF), ta kai sanssnin ‘yan ta’adda a Jihar Kaduna, inda ta kashe da dama daga cikinsu tare da ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su.
Kakakin NAF, Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya ce harin ya faru ne a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024, a karkashin Operation Farautar Mujiya.
- An Yi Bikin Kaddamar Da Shirin Zababbun Kalaman Shugaba Xi Jinping “Zango Na 3” Da Harshen Sifaniya A Peru
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Yadda ’Yan Peru Ke Fatan Ganin An Samar Da Salon Kasa Na Hadin Gwiwa
An kai harin ne a yankin Dunya Hill da Batauna Forest da ke karamar hukumar Giwa, inda ya kasance maboyar ‘yan ta’adda.
Aikin samamen auku ne bayan samun bayanan sirri da dakarun sojin suna yi, wanda ya ba su damar lalata sansanonin ‘yan ta’adda, makamai, da kayayyakin da suke amfani da su.
Rahotanni daga yankunan da abin ya shafa sun tabbatar da cewa da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere, tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
NAF, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da irin wadannan hare-hare don rage karfin ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Nijeriya.