Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta hana shigo da Indomie cikin kasar nan.
Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Litinin.
- Babu Wanda Zai Iya Rushe Masarautun Kano, Martanin Ganduje Ga Kwankwaso
- ‘Yan IPOB 9 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Kashe ‘Yansanda A Imo
Hukumar da ke kula da harkokin Nijeriya ta dauki matakin ne a daidai lokacin da hukumomin Taiwan da Malaysia suka gudanar da bincike, inda aka ce an gano sanadarin Ethylene oxide, wanda ke sanadin sanya ciwon daji a cikin taliyar.
A cewar shugabar NAFDAC, ta ce tuni Daraktan Kula da Ayyukan Abinci ya fara aiki kan hanyar bincike.
Sai dai ta yi alkawarin cewa za a bayyana wa ‘yan Nijeriya yadda ya kamata da sakamakon binciken.
Hukumar ta ce za ta fara daukar matakin hana bazuwar Indomie a kasuwanni daga ranar Talata.
A halin da ake ciki, kamfanin da ke yin Indomie, sun kare lafiyar kayayyakinsu, suna masu cewa duk wani nau’in takiyar ana sarrafa su ne bisa ka’idojin kiyaye abinci daga ka’idojin da Hukumar Indonesiya ta gindaya.
Kamfanin ya ci gaba da tabbatar da cewa duk samfuransa suna bin ka’idodin kiyaye abinci da ka’idodin a Indonesia da kuma sauran kasashe inda ake sayar da taliyar, “in ji sanarwar manema labarai da kamfanin ya fitar.