Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta ce za ta fara yaki da ‘yan kasuwa da masu hada man sauya launin fata domin kawar da su.
Mukaddashiyar babbar daraktar hukumar, Dakta Monica Eimunjeze, ta bayyana hakan, yayin wani taron karawa juna sani da NAFDAC ta shirya da hadin gwiwar ‘yan jaridu a fannin lafiya.
- 2023: Ana Rantsar Da Ni Zan Fara Sauya Fasalin Nijeriya – Atiku
- Honarabul Datti Babawo: Yadda Al’umma Ke Cin Gajiyar Shirinsa Na Bunkasa Kiwon Lafiya
Ta ce hukumar za ta fara amfani da karfin ikonta a kan shagunan siyar da kayan kwalliya da masu hada maya-mayan bilicin da basa kan ka’ida.
Dakta Monica ta kara da cewa a yanzu maza sun fi mata amfani da man bilicin wadanda ba a amince da su ba.
Nijeriya dai na daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna wajen amfani da mayukan da suke kodar da fata.