• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NAHCON Ta Bai Wa Jihohi Wa’adin Awa 48 Da Su Tura Kudaden Aikin Hajjin 2023

by Khalid Idris Doya
2 years ago
NAHCON

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta bai wa hukumomi, rassa-rassa da suke da ruwa da tsaki a harkar biyan kudin hajji tare da hukumomin da ke kula da jin dadin Alhazai na jihohi wa’adin zuwa ranar Juma’a su tura dukkanin kudaden kujerar aikin Hajjin 2023.

Shugaban hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, shi ne ya bayar da wannan wa’adin a jiya sa’ilin wata ganawa da manyan jami’an da ke kula da hukumomin kula da jin dadin Alhazai da sauran wadanda lamarin ya shafa da ya gudana a Hajj House, Abuja.

  • Hajjin 2023: Miliyan 3 Kowane Maniyyaci Zai Biya A Bana —NAHCON

A cewar sanarwar da mataimakiyar daraktan sashin yada labarai na hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce, zaman ya cimma muhimman batutuwa da suka dabaibaye shigar da kudaden kujerar aikin Hajjin ta hanyar da daidaitawa da shigar da adadin maniyyatan da suka cancanta suka dace da za su samu tafiya daga Nijeriya.

A cewar sanarwar ta hanyar hakikance adadin ne za a rattaba hannun yarjejeniya da jiragen da za su yi jigilar.

Hassan ya ce, hukumar za ta yi amfani ne kawai da adadin kudin mutanen da aka shigar zuwa asusun da aka ware daga ranar Juma’a kuma da adadin ne za a sanya hannun yarjejeniya da kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar zuwa Saudiyya Arabiyya, kan hakan, duk kudin da bai shiga ba kafin ranar Juma’a ba zai samu tafiya aikin hajji na 2023.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

Shugaban ya yi bayanin cewa da zarar suka kammala cike sharudan yarjejeniya ana sa ran za su biya kamfanonin jiragen da za su yi jigilar alhazan kaso 50 cikin 100 yayin da kuma wani karin kaso 35 zai biyo bayan an turo jiragen domin fara aikin jigilar.

Ya nuna damuwarsa kan yadda har zuwa yanzu ba a shigar da kudaden ba sakamakon daukan lokaci.

Shugaban na NAHCON din ya kuma ce duk wani shirye-shiryen da za su yi ba zai kammala ba har sai bayan tabbatar da adadin wadanda suka biya kudinsu da niyyar tafiya.

Idan za a tuna dai an sha dage lokacin amsar kudaden Hajjin hajji a lokuta daban-daban tun a watan Janairun 2023 ake kara wa’adin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
TCN
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Next Post
Zargin Yaudara: Wani Tela Ya Kashe Tsohuwar Masoyiyarsa A Kaduna

PSC Ta Kori Jami'an 'Yansanda 3 Kan Rashin Ladabi Da Biyayya

LABARAI MASU NASABA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.