Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ƙaryata rahoton da jaridar Newspoint Nigeria ta wallafa cewa Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi amfani da DSS wajen tsare wani ɗan jarida saboda rahoton da ya yi kan zargin shugaban da cin hanci.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ahmad Muazu, ya fitar, NAHCON ta ce labarin ƙarya ne da aka ƙirƙira don ɓata sunan hukumar.
- ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa
- Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe
Hukumar ta ƙalubalanci jaridar da ta kawo hujjoji idan tana da su.
Hukumar ta ce ba ta da hannu a harkar siyasa ko cin hanci, inda ta jadadda cewa shugabancinta na tafiya bisa tsarin gaskiya da bin doka.
NAHCON ta gargaɗi kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa labaran ƙarya.
A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.