Gwamnatin Najeriya ta ce tana goyon bayan ajandar jagorantar harkokin duniya da kasar Sin ta gabatar, inda ta kira ta “gudummawa mai dacewa da tunani” don karfafa tsarin kasa da kasa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya bayanna haka cikin wata sanarwar da ya fitar yau Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin Najeriya na maraba da manyan ka’idoji guda biyar na ajandar jagorantar duniya, wato “tabbatar da daidaito kan ikon mulkin kasa, bin dokokin kasa da kasa, aiwatar da ra’ayin bangarori daban-daban, kula da jama’a, da mai da hankali kan hanyoyin da suka dace”. Kuma ajandar ta yi daidai da manufofin ci gaban Najeriya, da tsarin cin gashin kai bisa manyan tsare-tsare, da kuma ajandar kungiyar Tarayyar Afirka ta 2063.
Sanarwar ta kara da cewa, “A matsayinta na daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Afirka, kuma mai taka rawa a harkokin diflomasiyya da ya kunshi bangarori daban daban, Najeriya ta dauki wannan ajanda a matsayin muhimmin dandali na inganta wasu muhimman al’amura da suka hada da yin gyare-gyare a MDD, da fasahar AI, da kuma kula da fannoni masu kunno kai kamar yanar gizo da sararin samaniya, ta yadda za a sa kaimi ga ci gaba cikin adalci.”(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp